Hankalin duniya ya karkata ne kan kalaman da ministan tsaron kasar Sin ya gabatar a taron tsaron kasashen Asiya a Singapore.
A jawabin sa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan tsaron kasar Li Shangfu, ya yi tsokaci game da kalubalen tsaro da ba a taba ganin irinsa ba a yankin Asiya da tekun Pasific.
Jami’in ya bayyana haka ne Lahadin nan a yayin taron tattaunawa na Shangri-La karo na 20, lokacin da yake bayani kan shawarar tsaro da kasar Sin ta gabatar.
Li ya bayyana cewa, tilas ne jama’a su nemi amsar wadannan tambayoyi: na farko wane ne ke kawo cikas ga zaman lafiya a yankin? Mene ne tushen yanayi na rudani da rashin zaman lafiya? Kuma me ya kamata mu yi taka-tsantsan mu kuma kiyaye?
Ya kara da cewa, wajibi ne a amsa wadannan tambayoyi bisa muradun tsaro, da kwanciyar hankali gami da makomar Asiya da tekun Pasifik.
Da kuma lura da cewa, wata kasa ta haifar da wani tsari na ‘juyin juya hali” da yakin basasa a yankuna daban daban, lamarin da ya haifar da hargitsi, ta kuma tafi ta bar rikici a baya, Li ya ce bai kamata a bar irin wannan abu ya faru a yankin Asiya da Pacific ba. (Ibrahim)