Hukumar Kula Da Shige Da Fice Ta Kasa (NIS) Reshen Jihar Rubas ta maƙala wa jami’inta 56 sabbin muƙaman da suka samu sakamakon ƙarin girma da aka yi musu.
Alƙaluma sun nuna cewa, jami’ai mata 29 da kuma jami’ai maza 27 ne suka amfana da ƙarin girman da aka yi a reshen hukumar na Jihar Ribas.
A jawabin da ya yi wa jami’in da aka kara wa matsayin Kwantirolan hukumar na jihar Ribas, James Sunday ya ja hankalinsu kan kara zage damtse don yin aiki tukuru da sadaukar da kai don yi wa kasa aiki kamar yadda hukumar ta dora masu nauyi.
Sunday ya bayyana cewa, duk wanda ya samu wani karin matsayi, shi ma ana sa ran samun kara mayar da hankali da jajircewa daga gunsa, musaman a yayin gudanar da ayyukansa ta hanyar kara nuna kwarewa.
A cewar Kwanturolan, a madadin kafatanin jami’in hukumar, “muna mika godiyar mu da kuma jinjinar ban girma ga ministan kula da harkokin cikin gida, wanda a karkashin shugabancinsa ne, aka fitar da wannan karin girman da aka yiwa jami’in da suka amfana da karin matsayin.”
Sunday ya ci gaba da cewa, har ila yau, muna mika godiyar mu ga Kwanturola janar na hukumar ta kasa da kuma jami’in kwamitin amintattu na hukumar bisa kokarin da suka yi, wajen ganin wannan karin matsayin da aka yiwa jami’an.
Ya yi addu’ar Allah ya ƙara wa Nijeriya ci gaba da shugabancin hukumar ta NIS da kuma reshensu na Jihar Ribas.