A kwanakin baya ne wakilan kungiyar tarayyar kasashen Larabawa suka kai ziyara a jihar Xinjiang, don ganewa idanunsu yadda al’ummar jihar mai wadata ke rayuwa, inda suka bayyana matukar jin dadinsu kan nasarorin da aka samu a kasar Sin, musamman babbar nasara da aka samu a fannin yaki da talauci.
’Yan tawagar sun bayyana cewa, jihar Xinjiang da suka gani da idanunsu, ta sha bamban da yadda wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya suka bayyana. Jihar Xinjiang, mai al’umma dake zaman jituwa, da tattalin arziki mai wadata, jama’ar dukkan kabilu suna zaune lami lafiya, kana ana kara yin ayyuka daban-daban.
Ban da wannan kuma, ’yan tawagar sun shaidawa taron manema labaran da aka shirya bayan kammala wannan muhimmiyar ziyara cewa, musulman Xinjiang suna da ’yancin gudanar da addini bisa doka, maganar cewa wai ana kisan kare dangi da zaluncin addini karya ce kawai aka kitsa da nufin bata sunan kasar Sin mai kaunar wanzar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a duniya.
Sanin kowa ne cewa, burin kafofin watsa labaran yammacin duniya shi ne, jirkita gaskiya game da kasashen da suke adawa da ko dai ci gaban su ko burinsu na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samun wadata a duniya baki daya.
Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, wani bangare ne na kasar Sin mai kunshe da kabilu daban-daban dake zaune cikin zaman lafiya da jituwa. Amma saboda adawa da jerin abubuwan dake faruwa da wadansu da ba su taba zuwa yankin ba, suke kokarin baza karairayi da yada jita-jita.
Daga ranar 30 ga watan Mayu zuwa ranar 2 ga watan nan ne, tawagar kungiyar kasashen Larabawa ta kai ziyara jihar Xinjiang, kuma sama da jami’ai 30 daga kasashen Larabawa 16 da suka hada da Masar, Saudi Arabiya, da Aljeriya da sakatariyar kungiyar Larabawa sun halarci taron.
Don haka, bai kamata mutane ko kasashe su rika fadin abin da ba su da masani a kai, don kawai neman biyan bukatunsu na siyasa. Domin zato zunubi ne, ko da ya kasance gaskiya. Kuma waka a bakin mai ita ta fi dadi. (Ibrahim Yaya)