Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023 ranar hutu domin tunawa da ranar dimokuradiyya ta shekarar 2023.
Babbar sakatariya ta dindindin ta ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade ce ta bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, inda ta taya daukacin ‘yan Nijeriya murnar wannan rana.
Ta ce “A wannan babbar rana mai tarihi, ana gayyatar ‘yan Nijeriya da abokan Nijeriya domin su taya Nijeriya murnar ci gaban da aka samu, su yi murna da irin nasarorin da aka samu, da kuma fatan samun kyakkyawar makoma ga dimokuradiyyar kasar.
“Babbar Sakatariyar na yi wa daukacin ‘yan Nijeriya fatan alkairi da murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya ta Nijeriya.”