Dan wasa Harry Kane yana cikin jerin ‘yan wasan da Real Madrid ke son zabar wanda zai maye gurbin Karim Benzema wanda ya tabbatar da barin kungiyar a wannan satin mai karewa.
Kane, mai shekara 29, yana da sauran kunshin kwantiragin kakar wasa daya da ta rage masa a Tottenham, wanda bai fayyace makomarsa ba kawo yanzu duk da cewa Manchester United tana zawarcinsa.
- Masana Da Jami’an Kasashen Sin Da Tanzania Sun Sha Alwashin Inganta Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe Masu Tasowa
- Shugabar Kasar Honduras Ta Fara Ziyara a Kasar Sin
Benzema wanda ya bar Real Madrid, bayan shekara 14 a Santiago Bermabeu, ya bar gurbin da kungiyar ya kamata ta cike kafin fara kakar badi kuma tuni kungiyar ta yi sallama da shi a ranar Lahadin da ta gabata a wasan kungiyar na karshe a La liga.
Sauran ‘yan wasan da Real Madrid ke son tuntuba sun hada da dan wasan Napoli, Bictor Osimhen da na Inter Milan, Lautaro Martinez da na Chelsea, Kai Habertz da kuma na Jubentus, Dusan Blahobic.
Real Madrid, mai kofin zakarun Turai 14 ta dade tana son daukar Kane, bayan da fitattun ‘yan kwallonta da yawa ke shirin barin Bernabeu a karshen kakar nan da aka kamala.
Bayan Benzema da zai bar Real Madrid a kakar nan, sauran sun hada da Eden Hazard da Marco Asensio da kuma Mariano Diaz wadanda tuni suka yi bankwana da kungiyar da magoya bayanta.
Idan wadannan ‘yan wasan suka bar Real Madrid, kungiyar za ta samu rarar Fam miliyan 77 da take biyansu ladan wasa da albashi da sauran tsarabe-tsarabe a kakar wasa guda daya.