Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso, ya ce a harkar gwamnati sun tattauna da Tinubu kan yadda za a iya yin aiki tare, to amma har yanzu ba su yanke shawarwari ba, sai bayan an ranstar da ‘yan majalisa za su ga yadda za a yi aiki tare.
BBC ta rawaiho cewa, Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya kuma jadada cewa batun tayin mukami da Tinubu ya yi masa suna kan tuntubar juna, kuma hakan ba wai yana nufin zai sauya jam’iyya ba ne, domin yana da tabbacin cewa gwamnatin hadaka Tinubu ke magana a kai.
- Yanzu-Yanzu Tinubu Na Ganawa Da Kwankwaso
- Rusau A Kano: APC Ta Bukaci Abba Ya Rushe Gine-ginen Da Kwankwaso Ya Sayar
Kwankwason ya ce nan da mako biyu za a fahimci inda suka dosa da shawarar da suka yanke.
Sannan ya mayar da martani a karshe kan kalaman Ganduje da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa da sunyi tozali da babu mamaki ya “mari Kwankwaso”.
Tsohon gwamnan ya ce wannan kalamai barazana ce wanda babu wanda ya isa ya kalle idonsa da irin wadanan maganganu.