A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, inda suka yi alkawarin inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu, da yin kira da a samar da kyakkyawan yanayi don ganin an warware rikicin kasar Ukraine.
Xi ya ce, Sin da Afirka ta Kudu, dukkansu manyan kasashe ne masu tasowa dake da muhimmanci, kuma dukkansu biyun, suna da alakar abokantaka ta musamman tamkar ‘yan uwa.
Shugaba Xi ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudu na da muhimmanci matuka wajen kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da jagorantar hadin kai da hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka.
Ya ce, a shirye kasar Sin take ta yi aiki tare da kasar Afirka ta Kudu, wajen inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu, da gina wata babbar al’ummar Sin da Afirka ta Kudu mai kyakkyawar makoma, da yin hadin gwiwa tare da tsakanin bangarori daban-daban, da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa, da tabbatar da tsarin kasa da kasa mai adalci da daidaito.
Xi ya kuma shaidawa Ramaphosa cewa, matsayin kasar Sin kan rikicin Ukraine bai sauya ba, wato inganta shawarwarin zaman lafiya.
Shugaban na kasar Sin ya ce, yana fatan dukkan bangarorin za su samar da kyawawan sharuddan warware rikicin ta hanyar yin shawarwari, kuma kasashe masu kaunar zaman lafiya a duniya da ke tabbatar da adalci, za su yi magana da murya mai ma’ana don inganta shawarwarin zaman lafiya. (Mai fassarawa: Ibrahim)