Kamfanin Kula da Albarkatun Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ya musanta ikirarin cewa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shugaban kamfanin, Mele Kyari.
Dangane da dakatarwar da aka yi wa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Godwin Emefiele a ranar Juma’a, an yi ta cece-kuce a shafukan sada zumunta na cewa an sauke Kyari daga mukaminsa.
- ANA Ta Bukaci Hadin Kan Kasa A Batun Shugabancin Majalisa Ta 10
- Sharhi A Kan Mata Marasa Wadatar Zuci
Sai dai a kamfanin ya musanta labarin a ranar Asabar ta hannun Garba Deen Muhammad, babban jami’in sadarwa na kamfanin NNPC, inda ya ce ikirarin ba gaskiya ba ne.
A cewarsa, “Wannan ba gaskiya ba ne.”
Idan za a tuna bayan dakatarwar da Tinubu ya dakatar Emefiele a ranar Juma’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp