Kungiyar koli ta kabilar Igbo, Ohanaeze Ndi Igbo, a ranar Asabar ta yi Allah wadai da dakatarwar da aka yi wa gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele, ta kuma bayyana hakan a matsayin wata kabilanci.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da daraktan kula da harkokin kasa na kungiyar, Mazi Chima Uzor, ya rabawa manema labarai.
- Tinubu Ya Dakatar Da Emefiele A Matsayin Gwamnan CBN
- DA DUMI-DUMI: DSS ta Karyata Cafke Gwamnan CBN Da Aka Dakatar
Kungiyar ta lura cewa dakatarwar Emefiele ba ta bi ka’ida ba, ta kara da cewa matakin na daga cikin kokarin gwamnatin mai ci da gangan da nufin kawar da ‘yan kabilar Igbo daga ofisoshin gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kungiyar Ohanaeze Ndi Igbo ta Duniya tana Allah-wadai da matakin dakatarwar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi wa, Dokta Godwin Emefiele, Gwamnan CBN.
” Wannan dakatarwar bata kan ka’ida, sannan kuma kama shi da DSS suka duk da umarnin kotu abin takaici ne kuma duk masu kishin Nijeriya wajibi ne su soki yin hakan” Muna kallon hakan a matsayin wani bangare na shirye-shiryen sabuwar gwamnati na kakkabe kabilar Igbo daga ofisoshin gwamnati.
“Wannan ba komai ba ne illa farautar da ake yi wa ‘Yan kabilar Igbo ba tare da wani dalili ba don sun nuna adawa da sabuwar gwamnati a zaben da ya gabata.
“Don haka muna rokon Shugaba Bola Tinubu da ya yi hattara da fara gwamnatinsa da ayyukan da za su iya jefa al’ummar cikin rudani.
“Ya kamata ya soke wannan shawarar da ba wa, Dokta Emefiele, damar kammala wa’adinsa na gwamnan babban bankin kasa maimakon kawo rudani da lalata dukkan tsare-tsaren da CBN ta gudanar a karkashin jagorancin Emefiele.”