Akalla mutune 21 ciki har da wani Fasto ‘yan bindiga suka hallaka a wani harin da suka kai cikin dare a kauyykan Rim, Jol, Kwi a Karamar Hukumar Riyom da kuma wani harin da suka kai a yankin Gana-Ropp da ke a Karamar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
‘Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Lahadi, inda kuma suka raunata wasu mazanuna kauyukan da dama.
- Da Dumi-Dumi: Abbas Ya Zama Shugaban Majalisar Wakilai Ta 10
- Sanata Barau Ya Zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa
Kakakin rundunar ‘yansanda na jihar, DSP Alabo Alfred, ya tabbatar da kai hare-haren biyu, inda ya ce, a lokacin harin na farko an hallaka Fulani biyu, harin na biyu kuma an yi sa cikin dare.
Ya ce, kwamishinan ‘yansandan jihar ya kai ziyara kauyykan da aka kai hare-haren biyu, ana kuma ci gaba da yin bincike.
An ruwaito cewa, maharan sun kai hare-haren ne, a lokacin da mzauna kauyukan ke barci.
Sakataren yada labarai na kungiyar matasan kabiliar Berom na kasa, Rwang Tengwong, na Berom, ya bayyana cewa, mutum biyu ‘yan bindigar suka kashe a kauyen Rim da ke a karamar hukumar Riyom, inda kuma aka kashe mutum bakwai a kauyen Jol, sai kuma mutune 11 a Kwi sai kuma wani Fasto mai suna Nichodemus Kim, da aka hallaka a kauyen Gana-Ropp da ke a karamar hukumar Barkin Ladi.
Harin na bayan nan dai, ya auku ne a ‘yan awanni bayan da wasu Fulani makiyaya biyu suna kan hanyarsu ta dawowa daga kiwo aka bindige su a yankin Fas da ke karamar hukumar Riyom da yammcin jiya Lahadi.