An farlanta wa Manzon Allah (SAW) yin Hajji a shekara ta shida bayan Hijira. Amma bai yi ba sai bayan Hijira da shekara 10.
Wasu malamai sun kawo hujjar cewa, bai yi Hajjin a shekara ta shida ba ne saboda a wannan shekarar Hajjin bai fado a cikin watan Zhul-Hajji ba. Haka nan a shekara ta bakwai, da ta takwas, da ta tara har sai a shekara ta 10 wanda a cikinta ne lokacin yin Hajjin ya zo daidai da watansa.
- Yanzu-yanzu: Babban Sufeton ‘Yansanda Ya Bada Umurnin Rufe Duka Sakataroriya 17 Na Jihar FilatoÂ
- Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Dakatar Da Shugaban EFCC, Bawa Har Illa-masha Allah
A shekara ta tara, bayan ya nada Sayyidina Abubakar (RA) a matsayin Amirul Hajji a cikin watan Zhul-kida, sai ya sanar da duniya cewa badi zai je Hajji, duk mai son zuwa ya zo ya bi shi ya ga yadda zai yi (SAW).
Malamai sun kara da cewa dalilin jinkirtawan har ila yau yana da alaka da al’adar da Larabawa suka kasance suna yi ta jujjuya Hajjin a watanni. Misali, idan a wannan shekarar an yi Hajji a watan Ramadan, badi sai su ce a watan Shawwal za a yi. A kan hakan, sai Annabi (SAW) ya jinkirta har zuwa shekara ta 10; lokacin da Hajjin ya fada a watan Zhul-hajji. Shi ya sa a ranar Arfa ya ce ya gode wa Allah duniya ta kewaya ta dawo wurin da aka halicce ta, dama Hajji a Zhul-hajji ake yi.
Imam Muslim ya ruwaito Hadisi wanda salsalarsa ke saduwa da Sayyidina Ja’afarus Sadik (RA) zuwa Babansa, Sayyidina Muhammadu Bakir (RA) cewa, “Mun shiga wurin Jabir bin Abdullahi, sai yake tambayar mutanen da muka shigo ko su wane ne; har dai ya zo kaina. Na ce ma sa ni ne Muhammadu Bakir dan Hussaini. Sai ya yi wawake ya dora hannunsa a kaina ya kama gashin kaina, ya kwance maballin rigata na sama sannan ya kwance na kasa, sai ya dora hannunsa a kirjina (don ya tuna irin kirjin Ma’aiki (SAW)), ni saurayi ne a wannan lokacin. Daga nan ya ce “lale da dan dan’uwana, tambayi abin da kake so. Na san kai malami ne, ilimi kake nema, so kake ka ji labarin kakanninka. Na zauna da Manzon Allah (SAW), na zauna da Sayyidina Aliyu, na zauna da Sayyidina Hassan da Hussaini, na zauna da Sayyidina Aliyu Zainul-Abidina (Babanka), don haka tambayi duk abin da kake so.” Shi (Jabir) makaho ne a lokacin, ina cikin tambayarsa kenan sai lokacin sallah ya yi, sai ya tashi a cikin wani dan mayafi da ya daura kuma ya yafa. Amma saboda kankancinsa duk lokacin da ya jefa shi a kafada sai ya fado alhali kuma ga babban mayafinsa a rataye a kantarsa. Sai ya yi mana sallah. Bayan gamawa na tambaye shi ya ba ni labarin Hajjin da Annabi (SAW) ya yi na karshe. Sai (Jabir) ya yi ishara da hannunsa tare da maganarsa, ya kure yatsunsa guda tara ya ce, “Annabi (SAW) ya zauna shekara tara bai yi Hajji ba, sannan ya yi izini a shekara ta 10 cewa zai yi Hajji a shekarar, sai mutane masu yawa suka taho Madina a shekarar ta 10, kowa yana so ya ga yadda Annabi (SAW) zai yi Hajji don ya yi koyi. Sai muka fita tare da shi (SAW) har muka zo Zul-hulaifa aka yi ta shirin harama. Sai matar Sayyidina Abubakar Asma’u bintu Umaisin ta haifi dan da ya sa ma sa sunan Annabi (Muhammadu bin Abubakar). Ta aika (jaririn) zuwa wurin Annabi (SAW) kuma ta tambaye shi cewa ga shi ta haihu, yanzu ya za ta yi (da batun Hajjinta)? Annabi (SAW) ya aiko mata da amsar cewa, “Ke ma ki yi wankan harama da Hajji, daga nan ki yi kunzugu (Nafkin, wannan yana nuna macen da ba ta tsarki idan za ta yi Aikin Hajji dole sai ta yi wankan harama duk da cewa ba za ta yi sallah ko ta shiga Ka’aba ba). Sai Manzon Allah (SAW) ya yi sallah a Masallacin Zul-hulaifa, daga nan ya hau rakumarsa (Kaswa) har ta daidaita da shi a sarari. Sai na duba sarari; ga mahaya nan da masu tafiyar kasa a ko ina dama da hagunsa (SAW) iya ganina. Annabi (SAW) kuma yana tsakiyar yara (matasa), sai ya yi niyya ya daga muryarsa yana cewa “Labbaikal lahumma labbaik… zuwa karshe”, (ma’ana amsawarka ya Allah, ka ce in je Hajji kuma na amsa). Mutane su ma suka amsa. Mu dai (in ji Sayyidina Jabir), Hajji kawai muka yi niyya a lokacin, a haka muka rinka tafiya tare da Annabi (SAW) har muka zo Makka muka shiga Masallaci. Farkon abin da Annabi ya fara yi bayan mun shigo Masallacin shi ne sumbantar Dutsen Hajarul As’wad. Sai ya fara Dawafi tare da sassarfa muma muna yi, har sai da aka yi zagaye uku sai (Annabi SAW) ya koma yin tafiya har aka yi zagaye hudu. Bayan haka, Annabi ya zo daidai Mukamu Annabi Ibrahim (AS) sai ya tsaya a bayansa, ya sa Mukamun a gabansa (tsakaninsa da Ka’aba), ya karanta ayar da ke cewa, “… Sai ku riki Mukamu Ibrahim a matsayin wurin Sallah”. Daga nan ya yi Sallar Nafila raka’a biyu, a ta farko ya karanta Kulya Ayyuhal Kafiruun, a ta biyu ya karanta Kulhuwallahu Ahad. Sai Annabi (SAW) ya koma ya sake sumbantar Hajarul As’wad. Daga nan ya fita zuwa kofar Safa, yayin da ya hau kan Safa sai ya karanta ayar da ke cewa, “Hakika Safa da Marwa alamomi ne daga alamomin Addinin Allah…” ya ce “Na fara da wanda Allah ya fara ambata”, da ya hango Ka’aba sai ya ce “La’ilaha illallahu wahdahu la shariykalahu lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli sha’in kadiyr. La’ilaha illallahu anjaza wa’adahu…” Sannan ya yi addu’a (idan Alhaji ya haddace wannan ya karanta, idan bai haddace ba ya karanta Subhanallahi wal-Hamdulillah wal-Lahu akbar ko ya yi ta fadin la’ilaha illallah). Bayan Annabi (SAW) ya gama addu’ar sai ya sake maimaita wannan addu’ar sau uku, sai ya sauko daga Safa ya taho Marwa. A lokacin da ya zo kwari (tsakiyar Safa da Marwa), sai ya yi sassarfa (a nan maza ke yin sassarfa, ban da mata). Da ya hau kan Marwa sai ya tsaya ya yi addu’a kamar yadda ya yi a Safa. Haka ya rika yi har ya kammala Sa’ayin a Marwa. Sai Annabi (SAW) ya ce “Idan na sa gaba kan abu ba na dawowa, da ban zo da abin hadaya ba, sai in yi Hajjin Tamattu’i in mayar da wannan Hajjin Umura. Amma yanzu duk wanda bai zo da abin hadaya ba, ya mayar da wannan Hajjin ya zama Umura (ya kwance haramarsa, ya yi aski)”. Sahabbai suka ce “Ya Rasulallahi bai fi kwana hudu a yi Arfa ba”, Annabi (SAW) ya ce “Ku cire haramar kawai, ku yi aski.”
“Sai Surakatu Ibn Malik Ibn Ju’ushamu ya mike ya ce “Ya Rasulallahi, wannan hukunci na yanzu (na mayar da Hajji Umura saboda rashin zuwa da abin hadaya), na wannan shekarar ne kawai ko na ko wace shekara ne?”, sai Annabi (SAW) ya shigar da yatsunsa wasu a cikin wasu ya dunkule su ya ce “Umura ta shiga cikin Hajji sau biyu, bari ma dai Umura ta shiga cikin Hajji har abada.” Sai Sayyidina Aliyu (RA) ya zo daga Yeman da rakuma, yana zuwa ya shiga wurin iyalinsa, ya tarad da matarsa (Sayyida Fadima (AS)) ta yi ado, ya tambaye ta game da hakan alhali ta riga ta yi harama da Hajji? Sai ta ce ma sa: “Babana (SAW) ya ce in yi.” Sayyidina Aliyu ya fada mana a Iraki (in ji Jabir) cewa, “Sai na tafi wurin Babanta don na kai kararta bisa abin da ta aikata kuma in tambaye shi (SAW). Da na fada ma sa, sai Annabi (SAW) ya ce “ta yi gaskiya, ta gaskiya. Kai me ka ce da za ka yi haramar Hajji?” sai na ce, “Cewa na yi; na yi niyyar harama da abin da Annabi ya yi harama da shi.”, daga nan Annabi (SAW) ya ce “Ni ina da abin hadaya, don haka ba zan warware harama ba”. Sayyidina Aliyu ya ce “to nima na zo da rakuma” sai Annabi (SAW) ya ce “to ka shiga cikin hadayata”, sai adadin rakuman da Annabi ya zo da su da wanda Sayyidina Aliyu ya zo da su suka kai yawan guda 100. Daga nan mutanen (da ba su zo da abin hadaya ba) duk suka warware Hajjinsu sai Annabi (SAW) kawai da wadanda suka zo da abin hadayarsu (Sayyidina Aliyu da wani Sahabi guda daya).
“Haka aka zauna har zuwa ranar takwas ga wata, sai Manzon Allah (SAW) ya hau rakumarsa zuwa Mina inda ya yi Sallolin Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i, Asubahi duk a can. Da gari ya waye bayan rana ta fito, Annabi (SAW) ya yi umurnin cewa a je a kafa ma sa rumfarsa a Arfa. Annabi (SAW) ya tafi Arfa ya shiga cikin rumfarsa, bai fito ba har sai lokacin da rana ta gota, sai ya bukaci a dora wa rakumarsa sirdi, ya hau aka biyo bayansa zuwa kwarin nan (wurin da Masallacin Namira yake a yanzu) ya yiwa mutane huduba… Bayan ya kammala sai Bilal ya yi wazna aka fara Sallah. Annabi (SAW) ya hada Azuhur da La’asar (Kasaru), daga nan ya hau rakuminsa ya dawo Arfa. Ya kalli Alkibla ya yi ta Zikiransa yana tsaye har zuwa lokacin da rana ta fadi. Sai ya sa Usamatu Ibn Zaidu ya hau bayansa a kan rakuminsa ya kama hanya yana tafiya ba tare da sauri ba yana mai nuni da hannunsa cewa mutane su tafi sannu a hankali, har aka zo Muzdalifa. Annabi (SAW) ya yi mana Magriba da Isha’i da kiran sallah daya, ikama guda biyu amma Isha’i kasru aka yi. Ana kammala sallar sai Annabi (SAW) ya kwanta ba tare da ya yi nafila ko daya ba har zuwa Asalatu. Sannan ya tashi ya yiwa al’umma Sallar Asubahi.
“Daga nan ya hau rakumarsa zuwa Mash’aril Haram (wani Masallaci kafin isa wurin Jifan Shaidan). Ya tsaya a nan yana Kabbarbari har zuwa lokacin da gari ya yi sarari, sannan ya mika hanya inda ya goyo Fadlu Dan Abbas a rakuminsa… Har suka iso Badnil Muhassar (wurin da aka hallaka giwaye) inda ya dan yi sauri har ya shige wurin ya bi ta hanyar da ake isa wurin Jifar Jamratul Akba ya yi Jifa da tsakuwa bakwai. Sannan bayan ya yi addu’a sai ya tafi wurin hadayarsa ya soke rakumi 63 da hannunsa, sai ya mika wa Sayyidina Aliyu mashi ya soke ragowar. Kuma ya yi horo a yanko nama kadan a ko wane rakumi aka dafa ya ci. Daga nan ya yi aski, sai kuma ya hau abin hawansa zuwa Makka ya yi Dawafin saukowa daga Arfa (Dawaful Ifada). Sannan ya yi Safa da Marwa. Bayan ya kammala sai ya je Rijiyar Zamzam, ‘ya’yan Abdulmuddalibi suka bashi guga ya sha.” Wannan shi ne ruwayar Hajjin Annabi (SAW) da Sayyidina Jabiru (RA) ya ruwaito.
Malamai sun yi bayanin cewa a cikin wannan Hadisin akwai hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda 100 a ciki. Za mu cigaba a kan darussan a karatunmu na gaba albarkar Annabi (SAW).
…Darussan Hadisin Aikin Hajjin Manzon Allah (SAW)
Wasu malamai sun bayyana cewa Hadisin yana dauke da karatuttuka da fa’idoji masu yawa a kan Hajji.
Malam Alkadiy Iyad ya ce malamai sun yi magana a kan hukunce-hukuncen fikihun da ke cikin Hadisin har sun rubuta littafai a kai. Hatta Abubakar bin Munzir ya yi babban juzu’i da ya fitar da hukunce-hukuncen Aikin Hajji sama da guda dari da hamsin a cikin Hadisin. Kuma ya kara da cewa da za a kara kula tare da zurfafa bincike a ciki, za a kara fitar da wasu hukunce-hukuncen.
Malamai sun ce akwai shiryarwa a cikin Hadisin cewa, yin wanka yayin haramar Hajji yana daga cikin sunna. Hatta ga matan da ba su da tsarki, masu jinin haila ko na haihuwa sunna ne su yi wannan wankan. Za a yi abubuwa na Hajji tare da su, sai dai ba za su shiga Masallaci ba, ba za su yi Dawafi ba. Amma za su je Arfa, su yi kwanan Muzdalifa, da Jifa.
Haka nan, Hadisin ya nunar da cewa yin kunzugu (nafkin) ga mai haila ko jinin biki sunna ne. Sannan za a yi harama da Hajji ne bayan an yi Sallar Farilla ko Nafila (ma’ana bayan mutum ya yi wankan harama ya sanya tufafi na harama, sai ya yi sallah idan lokacin farilla ne ko nafila sannan ya yi niyyar Hajjin). Kuma namiji zai daga murya yayin niyyar (ya yi a bayyane, ba tare da ya boye ba kuma bai cika wa mutune kunne ba).
Bayan haka, Hadisin ya nuna cewa ana so a tsayu a kan Talbiyyar da Manzon Allah (SAW) ya koyar: Labbaikal lahumma labbai…, amma Malamai sun ce idan mutum ya kara a kai ma babu laifi saboda Sayyidina Umar (RA) ya kara da: “Labbaika zanna ama’i wal-fadli alhasani, Labbaika marhuuban minka wa marguuban ilaika.”
Hadisin ya kuma koyar da cewa an so ga Alhaji idan zai fara Dawafi ya fara da sumbantar Hajarul As’wad. Sannan zai yi kewaye uku na farkon Dawafinsa da sassarfa (ba gudu ba kuma ba tafiya ba, tsaka-tsaki). Sauran kewaye hudun kuma zai yi da tafiya.
Wani abu da Hadisin bai kawo ba a nan (amma kuma akwai shi a shari’a) shi ne, idan namiji zai fara Dawafi ya shigo da mayafinsa ta karkashin hammatarsa ta dama, ya zama damtsensa yana waje, sai ya yafo shi ta kafadarsa ta hagu. Ma’ana damtsensa na dama yana waje, na hagu tare da hannunsa kuma suna cikin mayafin.
Bayan kammala Dawafi, sai mutum ya yi Sallar Nafila raka’a biyu a bayan Makamu Ibrahim (a yanzu an lullube wurin da Kwalbar Zinare), raka’a ta farko a karanta Fatiha da Kulya (Suratul Kafiruun), raka’a ta biyu Fatiha da Kulhuwallahu (Suratul Ikhlas).
Har ila yau, Hadisin ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunna ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu.
Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi. Mutum zai hau kan Safa har sai ya ga dutsen, da yake sun rufe shi da gilashi sai a matsa kusa da shi. Idan ya yiwu sai a kalli Ka’aba a ambaci Allah, sannan a yi addu’a. Za a maimaita haka sau uku.
Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka lahu sadaka wa’adahu wa nasara abdahu wa hadamal ahzhaba wahdahu”. Idan mutum bai iya ba, ya yi ta fadin La’ilaha’illallah. Sai ya yi addu’a.
Daga nan ya gangaro zuwa Marwa, a kan hanyarsa zai ga wani wuri da aka sanya koriyar fitila (tsakiyar Safa da Marwa), ana so ya yi sassarfa a wurin. Zai rika yin sassarfar a duk lokacin da ya zo wurin har ya kammala Sa’ayi, ba kamar sassarfar Dawafi da ake yi a kewaye uku ba kawai. Idan mutum ya hau Marwa, a can ma zai yi Zikiri ya yi addu’a.
Hadisin ya nuna cewa idan mutum ya kare Sa’ayi a kan Marwa, to ya kammala Umurarsa sai kawai ya yi aski amma ga mai Tamattu’i.
Bayan ya koma gida zai cigaba da harkokinsa na halas ciki har da kwanciya da iyali wadda aka haramta masa lokacin da ya yi harama har sai zuwa ranar Tarwiyya da za a yi niyyar Hajji.
Wani darasin Hadisin kuma shi ne, duk wanda ya warware haraminsa bayan ya kammala Umura, zai sake yin niyyar Hajji tare da fita zuwa garin Mina. Haka nan shi ma wanda bai warware ba (mai Hajjin Kirani) zai fita zuwa Mina. Sannan yana daga sunna mutum ya yi sallolin farilla guda biyar a can Mina (Azahar, La’asar, Magriba, Isha’i da Subahi). Kuma mutum zai kwana a Mina (daren ranar Arfa).
Haka nan sunna ce mutum kar ya fita zuwa Arfa har sai rana ta fito, kuma kar ya shiga Arfa sai bayan rana ta yi zawali (lokacin Azahar). Idan mutum yana da kokari, bayan an shiga Arfa sai ya tafi can Masallacin Namira ya saurari huduba; a yi Sallolin Azahar da La’asar da shi lokaci daya. Bayan kammala sallolin sai ya dawo Arfa (hukumomin can sun sanya alamomin da ke nuna kan iyakokin Arfa).
Yana daga sunna Liman ya yi huduba kafin gabatar da sallolin nan (Azahar da La’asar). Wannan ita ce huduba ta biyu, ta farkon ita ce wacce Annabi (SAW) ya yi a rana ta bakwai ga Zhul-Hijja. Akwai kuma huduba ta uku da Liman yake yi ranar Sallah, sai kuma ta hudu a ranar tafiya ta farko (kwana biyu bayan sallah).
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa bayan mutum ya dawo daga sallolin, zai dawo cikin Arfa ya tsaya a kan abin hawansa (idan yana da hali), don haka Annabi (SAW) ya yi. Idan bai samu ba, sai ya zauna ya cigaba da yin Zikiri da addu’o’i har rana ta fadi. Idan mutum ya samu hali ya je wurin da Annabi (SAW) ya tsaya, idan bai samu shi kenan, ko ina (inda aka shata) Arfa ne. Ana so a fuskanci Alkibla yayin tsayuwar ana addu’a. Babu laifi a je a ci abinci ko a dan yawata saboda gajiya duk dai a cikin kewayen Arfar.
Annabi (SAW) ya ce fiyayyen abin da ake karantawa ranar Arfa shi ne: “La’ila’ha’illallahu wahdahu lashariyka lahu lahul mulku wa lahul hamdu yuhyi wa yumiytu wa hul hayyu layamuutu biyadihil khair wa huwa ala kulli shai’in kadiyr”, guda 100.
Bayan an taso daga Arfa sai a nufi Muzdalifa cikin natsuwa ban da gaggawa. Annabi (SAW) ya rika jan akalar abar hawansa har kanta yana taba sirdi domin tafiya a hankali zuwa Muzdalifa. Hadisin ya kuma nuna mutum ya rika horon mutane da natsuwa a yayin komawa Muzdalifa. Da farko shi ya tabbatar da ya natsu, kana sai ya hori wasu da yin hakan.
Idan mutum ya isa Muzdalifa sai ya sauka a nan ya yi Sallolin Magriba da Isha’i a hade (Magriba cikakkiya, Isha’i kasru) ba kuma tare da yin nafila ba. Ana so da an kammala a samu wuri a huta kawai, kamar yadda aka ga Manzon Allah (SAW) ya yi.
Kwanan Muzdalifa na daga cikin sunna, amma an yi sauki ga marasa lafiya ko tsofaffi tukuf-tukuf ko mata masu kiba sosai da ake ji musu tausayin ba za su iya shiga jama’a ba masu yawa, duk sai su yi gaba don su yi Jifa da wuri kana su tafi Makka. Amma matukar mutum lafiyarsa kalau; kar ya yi gaggawa, ya tsaya ya kwana a nan Muzdalifa.
Hadisin ya kuma koyar da mu cewa sunna ce bayan mutum ya kwana a Muzdalifa bayan ya yi Sallar Asuba sai ya kama hanyar Minna zuwa Masallacin Mash’aril Haram ya dan jira zuwa wayewar gari sannan ya nufi wurin Jifa.
Idan mutum ya zo wurin da ake kira Badanil Muhassar sai ya dan yi sauri don a wannan wurin ne Allah ya halakar da Aburahata sa’ilin da ya zo zai rushe Ka’aba. Amma idan mutum bai san wurin ba shi kenan, dama shi wurin Jifa ya nufa.
A wannan ranar, Jifa daya za a yi na Jamratul Akaba da tsakuwa bakwai (wannan Hadisin ya nuna girman tsakuwar kamar na wake ko gyada wadda ko an samu wani ba za a ji ma sa ciwo ba). Duk lokacin da mutum ya daga hannu zai yi Jifar ya ce Allahu Akbar har ya kammala guda bakwan.
Yana daga falalar Jifar shaidan, Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya yi Jifa bai ji (a ransa) cewa an yafe masa zunubansa ba, to a sannan ne ma ya yi laifi.”
Daga nan idan mutum yana Hajjin Kirani ko Tamattu’i ne sai ya nufi wurin da zai yanka dabbarsa, idan ya gama ya yi aski sai ya nufi Makka don yin Dawaful Ifada.
Da zarar ya kammala Dawafin, to komai da aka haramta masa lokacin da ya yi harama ya halasta. Amma idan bai yi wannan Dawafin ba, an halasta ma sa sauran abubuwan da aka haramta wa mai Hajji, sai dai ban da kwanciya da iyali.
Bayan nan sai ya dawo Mina ya yi kwana biyu ko kwana uku. A yayin zaman na Mina kullum mutum zai yi Jifa uku. Daga nan Aikin Hajji ya kare, sai mutum ya je Makka ya yi Dawafin bankwana.
A takaice, wadannan su ne kadan daga cikin darussan Hadisin da Annabi (SAW) ya sanar da cewa duniya ta zo ta ga yadda zai yi Aikin Hajji a shekarar da ya fara yi (SAW).