• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shin Dakatar Da Godwin Emefiele Zai Farfado Da Tattalin Arzikin Kasa?

by Khalid Idris Doya
2 years ago
in Labarai
0
Farfado Da Burin Rage Amfani Da Tsabar Kudi A Tsakanin Al’umma
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A makon jiya ne, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele kuma nan da nan hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta cafke shi, domin amsa mata tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.

Godwin dai a karkashin kulawarsa, CBN ya fito da tsare-tsare da dama wadanda ake ganin sun janyo matsatsi a bangaren tattalin arziki da kuma takura wa jama’an kasa hada-hadar yau da gobe musamman batun sauya fasalin kudi a wani mawuyacin hali a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

  • Shugaba Xi Da Shugaban Falasdinawa Sun Gana A Birnin Beijing
  • An Daure Wata Mata Kan Yi Wa Yaro Dan Shekara 8 Fyade

Bisa dakatar da shi, masana sun fara harsashen shin ko za a samu tagomashin farfado da tattalin arzikin kasar nan biyo bayan matakin da ta Tinubun ya dauka.

A gabanin babban zaben 2023, Godwin Emefiele ya bijiro da sauya takardar kudi, lamarin da ya samu suka sosai daga bangarorin ‘yan kasa amma haka ya yi mursisi sai da aka aiwatar da tsarin, lamarin da aka sassauta bayan kammala babban zaben. Ko da yake, a lokacin yakin zaben kasar, Tinubu ya yi zargin cewa an bijiro da tsarin ne ma kawai domin kawo masa cikas a yayin neman kujerar shugaban kasa da yake yi.

Sai dai Emefiele ya ce sauya fasalin kudin wani yunkuri ne na yaki da rashawa da matsalar tsaro da kuma dabbaka tsarin rage amfani da tsabar kudi a tsakanin al’umma.

Labarai Masu Nasaba

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

A makon jiya ne dai Shugaban kasa Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN, Godwin Emefiele, nan take domin ba da cikakken damar gudanar da binciken da ake yi a ofishinsa da kuma matakin farfado da tsarin tattalin arziki.

Dakatar da shi ke da wuya kuma aka yada labarin cewa Emefiele ya shiga hannun DSS.

A sanarwar da ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fitar, ta ce an dakatar da Emefiele ne domin ba da cikakken damar a gudanar da binciken da ake yi a kan ofishinsa da kuma tsare-tsaren da ake kan yi wajen farfado da hada-hadar kudade na tattalin arzikin kasar nan.

Ko da yake sanarwar ba ta yi bayyana irin binciken da ake yi a kansa ba da kuma ranar da aka fara binciken.

Sanarwar ta ce, Emefiele ya mika ragamar tafiyar da harkokin ofishin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi, wanda zai kasance mai rikon kwarya har zuwa lokacin da za a kammala bincike ko sauye-sauyen da suka dace a yi.

Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ne ya nada Emefiele a matsayin gwamnan CBN a shekara 2014, kuma Buhari ya tafi da shi duk da zarge-zargen da aka yi masa har zuwa karshen mulkinsa, inda shi kuma Tinubu ya dakatar da shi mako biyu da hawansa kan karagar mulki.

Idan za a iya tunawa dai, a watannin baya ne kwamati na musamman da tsohon Shugaba Buhari ya kafa domin gudunar da bincike kan cajin cirewa da ajiyar kudi a asusun banki, sun yi zargin cewa kudaden da suka zarce tiliriliyan 89.09 da aka karkatar da su a karkashin jagorancin Emefiele.

Hon. Gudaji Kazaure, mamba a kwamitin ya yi zargin cewa dakataccen gwamnan babban bankin ya boye wasu tulin kudade da kuma ya ki ba su cikakken damar gudanar da bincike domin a gano hakikanain lamuran da ke faruwa.

Sai dai tun a wancan lokacin CBN ta karyata wannan zargin.

Zuwa hada wannan rahoton, dakataccen gwamnan CBN ya shafe kusan mako guda a tsare a hannun DSS, amma ana tunanin hukumar za ta iya gurfanar da shi a gaban kotu a kowani lokaci.

A dai watan Fabrairun 2023, DSS ta zargi dakataccen gwamnan CBN, Emefiele da tallafa wa ‘yan ta’addanci da kudade wanda hakan ya saba wa doka kuma laifi ne kan tattalin arzikin kasa.

A can baya dai an yi ta kai ruwa-rana tsakanin DSS da Emefiele, inda hukumar ta yi yunkurin kama Emefile sau tarin yawa, sai dai kotu ta taka musu burki, inda ita kuma hukumar ta dage cewa lallai akwai zarge-zargen da dole Emefiele ya amsa su.

A watan Fabrairun, hukumar tsaron ta ce, bincikenta na farko-farko ya nuna mata cewa akwai zargin hannu da take yi wa Emefiele na taimaka wa ta’addanci da kudade wanda hakan ya shafi manyan laifuka ga harkar tattalin arziki da ke barazana ga zaman lafiyan kasa.

Tun a wancan lokacin, DSS ta yi ta kokarin kama Emefiele amma kotun tarayya da ke zamanta a Maitama Babban Birnin Tarayya Abuja ta ba da umarnin hana kamashi.

A hukuncin da Alkalin Mai shari’a M.A Hassan ya nuna gazawar hukumar wajen gabatar da kwararan hujjojin da za su kai ga cafke Emefiele wanda a lokacin yana matsayin gwamnan babban bankin kasa.

A lokacin da Emefiele ya dawo daga kasar waje bayan shafe tsawon makonni a kasar waje, an jibge sojoji da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da DSS ba ta kama shi ba. Haka suka masa rakiya zuwa ofishinsa.

Tun ma kafin wannan kotun, ita ma babban kotun tarayya mai zamanta a Abuja ta ki amincewa da bukatar DSS na kamawa da tsare Emefiele a lokacin da yake matsayin gwamnan babban bankin kasa.

Wani mai suna US Gambarawa shi ne ya shigar da karar a madadin hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar 7 ga watan Disambar 2022 kan tuhumar mai lamba FHC /ABJ/CS/2255/2022.

Mai shari’a J.T Tsoho ya ce DSS ba ta gabatar da wata kwakkwarar shaidar da ta nuna dakataccen gwamnan CBN ya aikata laifin ba, sannan kamata ya yi a ce shugaba a wancan lokacin Buhari ya san da batun har ma ya sanya hannu kan bukatar kama Emefiele.

Har ila yau, idan za a iya tunawa Emefiele dai shi ma ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC, lamarin da tun a lokacin ana zarge shi da kwasan dukiyar ofishinsa wajen shiga harkokin siyasa da su.

Emefiele ya garzaya kotun Jihar Delta da ke zamanta a Kwale domin neman umarnin da zai hana babban bankin da hukumar zabe hanashi damar fitowa takarar shugaban kasa a 2023.

Sai dai hakarsa ba ta cimma ruwa ba, domin an fito baro-baro aka ce masa sai dai ya yi murabus idan yana son yin takarar fitar da gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC.

Babban jami’in gudanarwa na cibiyar ‘Centre for the Promotion of Pribate Enterprise (CPPE)’, Dakta Muda Yusuf, ya ce dakatarwar da shugaban kasa ya yi wa Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasa bai zo da mamaki ba lura da yadda Tinubun ya fito ya nuna sha’awarsa na farfado da tsare-tsaren da za su kyautata tattalin arziki da habaka darajar naira.

A cewar Dakta Yusuf, tun da farko Tinubu bai boye yadda yake ji kan wasu tsare-tsaren CBN ba, kuma kai-tsaye ya nuna rashin gamsuwarsa da wasu tsare-tsaren CBN a bangaren tsarin canjin kudade da na sauya fasalin kudi.

Kazalika, wani masanin tattalin arziki, Alhaji Mahdi Aminu, ya nuna fatan da suke da shi na cewa Tinubu zai dauki matakan da ake ganin za su kawo sauki ko farfado da tattalin arziki musamman a yunkurinsa na daga darajar naira.

Sai dai ya nuna fargabarsa na cewa duk da hakan, tulin basukan da suke kan Nijeriya ka iya zama barazana ga duk wani yunkuri na farfado da tattalin arziki. Ya kara da cewa matakin farko na dakatar da gwamnan CBN abu ne da zai ba da cikakken damar sanin inda ya kamata a dosa.

Kawo yanzu dai kallo ya kama sama kan batun Emefiele zuwa ga hukumar tsaron farin kaya ta DSS, inda ake tunanin hukumar za ta gurfanar da shi a gaban kotun kowani lokaci.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BuhariCBNDSS< DakatarwaTinubu
ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Na Maraba Da Kamfanonin Waje Da Su Zuba Jari Da Bunkasa Harkokinsu A Kasar

Next Post

Ya Zama Wajibi Sin Da Amurka Su Gina Alaka Da Juna Karkashin Salon Martaba Juna Da Daidaito

Related

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar
Manyan Labarai

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

2 hours ago
Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne
Labarai

Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

4 hours ago
Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)
Labarai

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

5 hours ago
Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari
Labarai

Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

6 hours ago
Labarai

Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu

18 hours ago
Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)
Labarai

Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)

19 hours ago
Next Post
Ya Zama Wajibi Sin Da Amurka Su Gina Alaka Da Juna Karkashin Salon Martaba Juna Da Daidaito

Ya Zama Wajibi Sin Da Amurka Su Gina Alaka Da Juna Karkashin Salon Martaba Juna Da Daidaito

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

Gwamnatin Tarayya Ta Gabatar Da Wasu Shirye-shirye Na Bunƙasa Kiwon Shanu

May 11, 2025
Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar

May 11, 2025
Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

Rashin Hadin Kai Ke Dakile Ci Gaban Masana’antar Kannywood -Ayatullahi Tage

May 11, 2025
Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

Barin Liverpool Ita Ce Shawara Mafi Wahala Da Na Taɓa Yankewa A Rayuwata -Alexander 

May 11, 2025
Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

Shugaban NPA Ya Sha Yabo Kan Yadda Ya Bunƙasa Tashar Jiragen Ruwa Ta Onne

May 11, 2025
Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

Tarihin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (5)

May 11, 2025
Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

Kaduna Ta Gano Ma’adanai 73, Yayin Da Take Neman Masu Zuba Jari

May 11, 2025
Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

May 10, 2025
An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

An Fara Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Na Matakin Koli Tsakanin Sin Da Amurka A Geneva

May 10, 2025
Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

Sharhi: Sin Da Rasha Suna Sauke Nauyin Dake Wuyansu

May 10, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.