Yayin wata ziyara da jakadun kasashen Afirka 33 suka gudanar a birnin Nanjing, fadar mulkin lardin Jiangsu dake kasar Sin, tsakanin ranaikun 13 zuwa 14 ga watan Yunin nan, sun bayyana gamsuwa game da yanayin bunkasar al’adun gargajiya, da ci gaban da lardin na Jiangsu ya samu, da ma kyakkyawar makoma da suka ce hadin gwiwar Sin da Afirka ke da shi a nan gaba.
Kaza lika sun sha alwashin ingiza fahimtar juna, da hadin gwiwa da lardin, ta yadda za a kai ga zurfafa ci gaban dangantakar abokantaka da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka daga dukkan fannoni.
Yayin da ya ziyarci kamfanin CRRC Nanjing Puzhen, jakadan Najeriya a Sin Ambasada Baba Ahmad Jidda, ya jinjinawa kamfanin, bisa yadda yake taka rawar gani a fannin raya shawarar “ziri daya da hanya daya”
tsakanin Sin da kasashen Afirka.
Jakadan ya ce kamfanin CRRC, ya samar da kayayyakin amfani a layukan dogo dake Najeriya, da ma sauran kasashen Afirka da dama, matakin da ya yi matukar bunkasa hadin gwiwar Sin da sauran kasashen Afirka.
Daga nan sai ya bayyana matsayar Najeriya, ta ci gaba da mara baya ga hadin gwiwar lardin Jiangsu da kasashen Afirka, a fannin karfafa hadin gwiwa a fannonin sarrafa hajoji, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, tare da fatan kamfanonin dake Jiangsu za su yi amfani da fifikon su na fasahohin zamani, wajen cin gajiyar manyan kasuwannin nahiyar Afirka a nan gaba. (Saminu Alhassan)