A jiya ne, wani kakakin ofishin yankin Hong Kong na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi Allah wadai da wani kudurin da majalisar dokokin nahiyar Turai ta fidda.
Kudurin dake goyon bayan wadanda ke neman bata yanayin zaman lafiya a yankin Hong Kong, da neman kakabawa jami’an gwamnatin tsakiyar kasar Sin da na yankin Hong Kong takunkumi.
A cikin wannan kuduri, majalisar dokokin nahiyar Turai ta yi katsalandan kan harkokin Hongkong da harkokin cikin gidan kasar Sin, gami da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa, saboda haka Sin ta yi Allah wadai da shi.
Kakakin ya ce, ‘yan siyasan majalisar dokokin nahiyar Turai suna shafa bakin fenti kan dokar tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong, da sauran dokokin yankin Hong Kong, bisa hujjar “kare hakkin dan Adam”, da “dimokuradiyya”, da kuma “’yancin kai”, domin cimma mugun burinsu a fannin siyasa.
Ya kuma jaddada cewa, wadannan ‘yan siyasan kasashen wajen, ba za su hana aniyar gwamnatin yankin Hong Kong wajen aiwatar da harkokin yankin bisa doka, da hukunta wadanda suka aikata laifuffuka ba, kuma, ba za su iya bata aniyar gwamnatin tsakiyar kasar Sin da gwamnatin yankin Hong Kong na kasar Sin wajen tsaron kasa ba, balle ma, hana ayyukan aiwatar da manufar “kasa daya, tsarin mulki iri biyu”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)