A jiya Jumma’a ne zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar Mali da su warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar tattaunawa, da samar da kyakkyawan yanayi don gudanar da kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar da za a yi a ranar Lahadi.
Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Zhang Jun ya bayyana cewa, kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar ta Mali, wani muhimmin mataki ne na kiyaye tsarin mika mulki da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa. Kasar Sin na maraba da ci gaban da aka samu a kasar Mali wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar, da shirye-shiryen gudanar da kuri’ar raba gardamar, da kafa hukumar kula da harkokin zabe.
Zhang ya kara da cewa, kuri’ar raba gardama kan kundin tsarin mulki lamari ne na cikin gida na Mali. Ya kamata kasashen duniya su mutunta ‘yancin kasar Mali da ikon mallaka.
Kasar Sin na kira ga kungiyoyin yankuna masu ruwa da tsaki da su karfafa tuntubar gwamnatin kasar Mali, da kuma taka rawa wajen nuna goyon bayan tsarin mika mulki a tafarki na siyasa a kasar Mali. (Yahaya)