A ziyarar da ya kai kasar Sin a baya-bayan nan, shugaban kasar Falasdinu Mahmoud Abbas ya shaidawa wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, sanarwar da kasar Sin ta bayar na kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, za ta ba da karfi ga ci gaban al’ummar Palasdinu.
Abbas ya ce ziyararsa a kasar Sin na da matukar muhimmanci. Bangaren kasar Sin ya sanar da kyautata huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, hakan zai karfafa gwiwar al’ummar Palasdinu, kuma kullum kasar Sin na tsayawa tare da al’ummar Palasdinu. Ya kuma amince da duk shawarwarin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar dangane da daidaita batun Palasdinu.
A ko da yaushe kasar Sin tana tsayawa tare da al’ummar Falasdinu, a matakin shiyya-shiyya da na kasa da kasa, musamman ma a Majalisar Dinkin Duniya da kwamitin sulhu.
Yanzu shekaru da dama ke nan, kasar Sin ba ta taba canza matsayinta gami da Falasdinu ba. (Yahaya)