Shida daga cikin dalibai bakwai na jami’ar Jos da aka yi garkuwa da su, sun tsira bayan shafe kwanaki biyu a hannun masu garkuwa da mutane.
Daliban wadanda suke rayuwa a kusa da makarantar a daren ranar Laraba da daddare ne ‘yan bindigan suka kutsa kai cikin dakunansu da ke kan hanyar Bauchi ta layin Ring da ke karamar hukumar Jos ta arewa inda suka yi awun gaba da su.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7
- Dan Majalisar Dokokin Jihar Legas, Abdulsobur Omititi Ya Rasu A Wajen Taron Tinubu A JosÂ
Kwamishinan ‘yansandan jihar Filato, shi ne ya sanar da batun kubutar daliban a wata sanarwar da ya fitar, ya ce, rundunar tana kan kokarin ceto sauran dayan dalibin.
Sanarwar ta ce, “A yau, rundunar ‘yansandan jihar Filato tana farin cikin sanar da al’umma cewa biyar daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su a ranar 13/06/2023 sun samu ‘yancinsu.
“Rundunar ta dauki matakan gaggawa tun lokacin da ta samu labarin garkuwan kuma bisa aiki tukuru da sashin yaki da masu garkuwa da mutane, iyalan wadanda lamarin ya shafa da al’umma domin tabbatar da an kubutar da daliban.
“Daya daga cikin daliban ya tsere daga hannun masu garkuwan, har yanzu kuma akwai sauran mutum daya a hannun masu garkuwan. Adadin wadanda suka kubutar zuwa yanzu su shida (6) ke nan.
“Kazalika, kwamishinan ‘yansanda Bartholomew N. Onyeka ya bayar da umarni ga kwamandan yankin Metro da babban baturen ‘yansansa (DPO) a caji ofis din Nasarawa Gwong da su tabbatar sun ceto dayan dalibin daga hannun masu garkuwan tare da kamosu domin su fuskanci hukunci daidai da laifinsu.”
Kwamishinan ya nanata aniyar hukumar na kare rayuwa da dukiyar jama’an jihar a kowani lokaci, ya nemi hadin kansu a kowani lokaci domin cimma nasarar kyautaya tsaro.