Barkanku da kasancewa tare da shafin Taskira, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma. Tsokacin mu na yau zai yi duba ne game da wasu matsaloli wanda Mata ke fuskanta a wajen mazajensu yayin da suke dauke da juna biyu ko kuma bayan haihuwa. Idan aka yi duba da matan da ke zuwa asibiti domin rainon ciki (Awo) ko haihuwa, za a ga mafi yawan mata na fuskantar kalubale na rashin kulawar da ya kamata mazajensu su ba su a yayin da suke dauke da juna biyu ko lokacin da suke yunkurin saukewa. Mafi yawan maza na kin bawa matansu kulawar da ta dace musamman wajen siyen magunguna ko ba da kudin hoton ciki, da dai sauran abubuwan da suka kamata a yi wa matar a asibiti. Akwai abubuwa da dama wanda wasu mazan ke bi dan cutar da matansu yayin da suke dauke da ciki tamkar cikin ba nasu ba ne, wani asibitin ma ba zai bar matar ta je ba in kuwa ta je to a boye ne. Wani kuma zai bar ta ta je amma fucikarsa ba za ta yi magani ba, kuma yana da shi ba wai babu ba, wani namijin kuma a kullum ba shi da aiki sai duka ko zagi, tsana ta shiga tsakani sabida tana dauke da ciki, kamar wadda ta fita tayyo.
Wani idan matarsa za ta haihu a lokacin za a neme shi a rasa ko a waya ba za a iya samunsa ba, sabida biyan kudi da sauran abubuwan da za a iya bukata alhalin yana da kudin, wani ma sai dai ta ji labarin cewa daga asibitin ta wuce gidansu ya saketa, ba don komai ba sai dan yana jin nauyi ya karu akansa, wanda inda za a buncika wani ko ta nemi tayi tazarar haihuwa ba zai taba bari ba, amma kuma duk haihuwa da rainon ciki haka take fama a wajensa. Dalilin hakan ya sa shafin Taskira jin ta bakin wasu daga cikin mabiyansa game da wannan matsala, Ko laifin waye tsakanin Mijin da Matar? Me yake janyo hakan kuma ta wacce hanya za a magance matsalar? Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
Sunana Princess Fatimah Zahra Mazadu Gomben Lanjeriya:
Gaskiya abun da zan ce ya buwayi duniya dan mazajen yanzu rayuwa suke da auren sha’awa yawanci. Mafi akasarin maza basa murna da yawan haihuwa wannan haka ne ‘more especially’ in an haifi ba abun da suke so ba, misali namiji yake so kika haifi mace. Ciki wasu mata suna kurewa maza maleji ne da munafunci da son tara abun duniya ta hanyar langwabewa yau jinya gobe ciwo, wasu kuma kazantar banza da rashin kulawa da miji. Dukkansu dan kai kayi cikin bai kamata ka nuna kyama ba, ita ai mace in ka ga ba ta son haihuwa toh rashin rabon gaggawa ne, ko shi mijin dan son rayuwa ne dole ta dakata in bata son komawa gidansu. Hanya daya ce in baka son haihuwa kar ka yi aure, dan ba wanda bai sha’awar ajiye zuriya, kai da ba a haihuwa za a haife ka? Dan a zahiri wallahi mata basu cika kin haihuwa ba, sai dai maza su yaudare su su bata musu rayuwa na har abada da kwayoyin hana haihuwa. Allah ya shirya su, amma kira na ga mata da ki rasa mahaifarki ko ki lalata rayuwar ki gwara ki ji kunyar mutanen duniya ki dawo zawarci Allah zai baki mai son tara zuriya, in fannin namiji ne ya kiyaye dan ba dawwama za ka yi a duniya ba, kana son mai maka addu’a da wanda za ka barwa duk wata amana ta rayuwa, ciki wahala ne dan Allah maza ana tausayin mata, wallahi ka ga mace na tafiya wata sai ka zubar mata da hawaye, wata kuma in tana bed rest sai ka tausayamata. Ku ji tsoron Allah ku ji tausayin matanku ko dan gobe kiyama su yi alfahari da ku, mata a daure dan kin yi ciki ba zai hana ki yi wa mijinki biyayya ba ko dan lahirarki tayi kyeu. Muhayyafa mu cika umurni da fadin Manzon Allah (S. A. W).
Sunana Mas’ud Saleh Dokatawa:
Wannan halayen banza abu ne mara kyau, sannan rashin sanin hakkin aure ne, kuma ya sabawa al’adar malam bahaushe, idan mutum bai yi wa matarsa abin da ya zama wajibi ba na kula da lafiya daga daukan ciki har zuwa haihuwa ba, lallai zai gamu da fushin Allah. Sannan ba zai ga da kyau ba shi ma saboda rashin sauke nauyin da Allah ya dora masa matukar yanada halin yin hakan, sannan ko ba da kudi ba akwai kulawa ta daban wacce zai iya yi. Laifin na maza ne, indai ba cikin shege bane ai bai kamata maza su yi wa matan haka ba. Abin da ke jawo hakan shi ne; Wasu matan sukan zama kazamai idan cikinsu yayi girma basa iya tsabtace jikinsu da muhallinsu. Sannan wasu mazan sukan yi hakanne saboda ba a son ransu matan suka dauki cikin ba don haka suke yi musu wulakanci, wasu mazan kuma suna zargin matan akan cikin ya sa suke gudarsu har bayan haihuwa. Hanyar magancewa shi ne; Maza su ji tsoron Allah su sani cewa za a tambayesu akan duk abin da aka basu kiwo, su kuma matan su rinka kulawa da kansu akan tsafta da kula da jikinsu da kuma kaucewa dukkan abin da zai iya kawo zargi a tsakanin zamansu. Shawara ita ce su ji tsoron Allah su daina, sannan kuma su kiyaye hakkokin iyalensu kada suyi abin da zai batawa matansu rai da gangan, sannan mata suna da bukatar kulawa a koda yaushe.
Sunana Musbahu Muhammad Gorondutse:
Rashin tausayi da cikakken ilimin addini dana zamani shi yake haifar da haka. Laifin miji ya fi yawa, amma sai dai suma matan ya kamata su duba a inda suka gaza su gyara kuma su dinga yawaita addu’a. Namiji ya kamata ya san cewa ita matar amanar Allah ce a hannunsa dan haka duk abin da yayi mata sai Allah yayi musu hisabi, kuma ya tuna shi ma zai iya haifar ‘ya Mace ba zai so a yi wa ‘yarsa hakan ba. Shawara su ji tsoron Allah su daina hakan, sabida farin cikin matar shi ne farin cikinsa. Sannan su kansu ‘ya’yansu sai sun fi kaunarsa idan suna zaman lafiya da matarsa.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, Marubuci, Dan Jarida, daga Jos ta Arewa, a Jihar Filato:
Na so in yi sharhi kan wannan muhimmin darasin, saboda abu ne da ya dade yana ci min tuwo a kwarya. Wasu maza masu aure suna yin wasu abubuwa da za a iya fassara shi da rashin kulawa, rashin nuna kauna, da rashin nuna dattako ga matansu, musamman a lokacin da suke cikin lalurar rashin lafiya, ko yayin haihuwa. Duk wani magidanci ya san irin dawainiya da kokari da mata ke yi a cikin gidaje da dakinansu na aure, wajen kula da iyalansu, tarbiyyar yara da hidimar kula da bukatun maigida. Don haka a duk lokacin da Allah ya jarabce su da wata lalura ta rashin lafiya, mu nuna musu tausayawa, tattali, da taimaka musu, wajen taya su wasu ayyuka ko dauke musu wasu É—awainiyoyin har su samu lafiya. A duk lokacin da suke dauke da juna biyu mu tabbatar da mun ba su kulawa ta musamman, daga abin da za su ci, yadda za su kula da kansu, da kuma uwa-uba zuwa asibiti domin yin awu da duba lafiyarta da jaririn da za ta haifa. Kuskure ne babba a ce ba ma nuna damuwa ga wannan muhimmin bangare, alhalin mu ne muka sa su cikin laulayi da dawainiyoyin da suke fama da su na rainon ciki. Haka kuma yana da muhimmanci sosai, idan lokacin haihuwarta ya yi maigida ya kasance kusa da ita, don ba ta kwarin gwiwa da nuna mata kulawa, har ta samu kanta lafiya. Kuma mu yi iya kokarin mu wajen ba ta kulawar da ta kamata, na lafiya da abin da za ta ci ta samu kwarin gwiwar shayar da abin da ta haifa. Ba koyaushe ba ne kudi ke ya ye damuwa, amma nuna kauna da kulawa, da bai wa mutum muhimmanci yana sa ya ji a ransa lallai yana da bangon jingina, kuma ana son shi. Wannan kuma ya hada har da su matan, domin akasarin korafin da maza ke yi shi ne, mata ba sa yabawa da kokarin da suke yi, duk fafutuka da sadaukarwar da suke yi a kan hidimar iyalinsa, matansu na rainawa. Ba sa yaba musu, har ma da cewa ai hakkinsu ne, ba sa bukatar a yi musu godiya. Gaskiya wannan kuskure ne, don ko Allah Ubangiji ya ce da bayinsa idan kun gode min zan kara muku!. Ya kamata mu rika yabawa da kokarin juna da nuna kauna da tausayawa a kowanne hali.
Sunana Deejat Thani daga Jihar Niger, Minna:
Idan za a fadi gaskiya in akwai so da kauna, tausayi da kuma ilimi, ai mace mai ciki abin tausayi ce a gun kowa bare mijinta. Tare kuka yi babyn nan toh ko ma menene ya kamata ace zuciyarka tana ciki da tausayin ta, in babu soyayya akwai tausayi. In kuma da ilimi duk saura mutum ba zai rasa su ba, dan ko tunani hakkinta da ke kanka ya isheka ka saukaka mata wahalar. Gaskiya laifinsu ne su biyu, abin da za a kira hakan wasu za su ce yahudanci amma a gani na wannan dabara ce. Kafin kuyi aure akwai abubuwa da dama da ya kamata ta yi yarjejeniya akai ku kuma kuyi magana akai cikinsu kuwa har da lokacin daukan ciki, guda nawa kuke su da yadda za ku dauki nauyinsu, ‘like’ in kun kawo irin wannan maganar rayuwan ki will be in balance, sai kuyi abinku tare. Musamman ma da cewa akwai hanyoyin taimakawa ga faruwan hakan. Gaskiya rashin ‘communication’ magana tsakanin ma’aurantan ke janyo matsalar nan. Komai kankantar
magana ku zauna kuyi shi gudun kar ya girma ya zama babba kin san me yake so, yadda yake so, yadda za ku ciyo kan matsalar dan kar aji bakinku. Shawara na gare ku masu dabi’un nan shi ne; kusa wa zuciyar ku hakuri babu abin da ya fi karfin Allah, idan kuma kagan abu ya same ku, ka kaddara haka yake rubuce a littafinka. Mu nemi ilimin abubuwa kafin mu yi su, kar mu biye wa wannan haka yayi, ni ma haka zan yi.
Sunana Ibraheem Ismail Ibraheem daga Jihar Kano:
Rashin sanin darajar mace ce da kuma rashin adalci, yin hakan yana jawo rashin zaman lafiya, da rashin mutunta juna, Laifin na maza ne masu irin wannan halayyar, yadda za a magance shi ne; Gyrawa ta hanyar kyautatawa, Allah ya sa za mu ji mu gyara.
Sunana Abdulrrashid Haruna daga Jihar Kano Nassarawa LGA:
Gaskiya wannan ba komai bane face sakaci da rashin kula, wanda hakan ba karamin cutarwa bane a zamantakewar miji da mata, sannan hakan ya sabawa amanar ta da aka baka kuma Allah ba zai bar duk mai wannan hali ba, dan farali ne ga miji kula da matarsa. Laifin Miji ne,abin da ke janyo hakan ayi Auren ba tare da yana santa ba, Ma’ana ya zama dama can ita ce take san shi, ko ya zama Auren dole aka yi musu. Gaskiya shawara gare su su ji tsoran Allah su tuna Allah bai ce ayi Aure ba muddin ba za a yi adalci ba.