Rashin shugabanci ko jagoranci nagari a wannan nahiya tamu ta Afurka, na daga ababen da suka zame mana mujazar rashin amfanuwa daga basukan ketare da shugabannin kasashen na Afurka, ciki har da Nijeriya ke kan ciwowa daga Turawan na yamma zuwa kasashensu.
Babu shakka, ciwo irin wadancan basuka daga kasashen na Turai, na da bukatar yin taka tsantsan ne ainun ainun! Ko kadan, a duk sa’adda muka wawuro basukan daga gare su, ba su yi mana fatan mukai ga samun ikon sauke wannan nauyi na bashi, ma’ana, ba sa fatan mu iya biya. Sai aka wayigari zani ce ta tadda mu je mu, tun da dama, mu ma shugabannin namu, ba su ciwowa da niyyar su biya salun alun. Tuni, irin yadda suke mu’amalantar wadancan madudan kudaden da suke ciwo mana bashin nasu ne ke fassara rashin wani katabus daga janibinsu, na son gamawa lafiya da tarago tarago na basukan da suke yin habzi da su, cikin yanayi na kekashewar zuciya!.
- Mace Aba Ce Mai Daraja, Ba Sai Ta Ba Da Kanta Ba Za Ta Yi Suna A Fim – Jamila Saleh
- Gwamnatin Neja Za Ta Fito Da Tsarin Ci gaban Jihar Na Shekaru 30
Na daga miyagun ka’idoji da irin wadancan masu ba da bashi ko lamuni ke amfani da, a duk sa’adda Kasar da ta ciwo bashin nasu ta afka yanayin “sobereign default”, wato ta gaza biyan bashin. Daga nan ne kuma za su dukufa suna masu bijirarwa da wannan Kasa wasu irin salo salon da, ba tare da daukar wani lokaci mai tsawo ba, Kasar za ta durkushe ne kacokan ta fuskar tattalin arziki, ko kuma radadin talaucin da suke ciki a yau, ya kara munana matuka!.
Wani lokaci da Bankin Lamuni na Duniya, IMF, ya shake wuyan tattalin arzikin Kasar Argentina, sakamakon tsirin bashi da suka ciwo daga Bankin, a karshe suka gaza biya. Sai Bankin ya nemi Kasar na ta daina buga takardun kudaden da da su ne take biyan ma’aikata albashi a duk karshen Wata. Ke nan dai, burin IMF shi ne, a wayigari ma’aikatan lafiya, ilmi, gobara, gona da makamantansu duka su tsunduma cikin yajin aiki, eh mana, tun da albashi ya tsaya cak! Daga nan kuma mene ne ake tunanin zai biyo baya? Cutuka ne za su barke a Kasar! A yi ta kyankyashe jahilan mutane tun da babu zuwa makaranta, kuma samun abinci ma zai faskara ne a hankali a hankali.
A fili ne yake cewa, yayinda ya zamto Argentina ta biyewa Bankin na IMF, ta kauracewa buga kudaden albashi, to da sannu za a zo gabar da jama’ar Kasar za su yi wa gwamnati bore ne. Daga nan ne kuma, sai Turawan su kara dankarawa Kasar mamakon basuka, ta hanyar saida musu da makaman da za su murkushe ‘yan tawaye bashi. Bugu da kari kuma, ko dai Turawan su shigo cikin Kasar da kansu, ko kuma su hada-kai da wasu marasa kishin kasa, wajen cin moriyar wannan rikici da Kasar ta afka ciki, tare da yunkurin sace wasu mu’adanan Kasar.
Cin Bashi Na Jaza Korar Ma’aikata
Ko ba a yi wani karin bayani ba, wancan yanayi da IMF ta yi kokarin zurma Kasar Argentina ciki, ya ishi mai karatu yin iznar yiwuwar haifar da rashin aikin-yi a Kasa. Babu shakka rungumar bukatar ta IMF, la budda sai ya jefa Kasar cikin mummunar kangin rashin aikin-yi. Ba ya ga Argentina, ya faru ma a Kasar Zambia, sa’adda suma suka ciwo bashin ketare iya-wuya. Sai hakan ya jaza rufe dubban masa’antunsu a Kasar cikin Shekarar 1990, lokacin mulkin shugaba Kenneth Kaunda. Sanadiyyar masifar kangin bashin da mutanen Kasar Zambia suka samu kansu ciki, sai suka yanke shawarar kayar da Kaunda a zaben Shekarar 1991, tare da mayegurbinsa da sabon shugaba Frederick Chiluba, da niyyar ko za a sami wata faraga da walwala a Kasar. Amma maimakon lamura su gyaru a Kasar, amma lamura ma sai kara ta’azzara ne suke dada yi (Analysis, Bol. 1, No. 1, July, 2002 : 36).
Sabon shugaba Chiluba, ya gaji rayaiyun kamfanonin kayan sawa, wato masaku, har kimanin guda 140 sa’adda ya amshi karagar mulki daga Kaunda. Amma, sa’adda ya kammala zangon mulkinsa na biyu, sai wadancan masaku suka dawo guda takwas (8) ne kacal. Lazim ne, a duk sa’adda bashi yai wa wata Kasa katutu, kawai, wai don an canja sabbin shugabanni a Kasar, muddin idan ba a tasamma hanyoyin biyan wadancan basuka ba, sai an ji jama’ar Kasar sun dawo suna masu nuna soyaiyarsu ga wancan tsohon shugaba, wanda shugaba na yanzu ya gada. Irin wannan yanayi na kwan gaba kwan baya, na daga abinda ke ciwa ‘yan Nijeriya tuwo a kwarya. Duk shugaban da ya tafi, duk sharrinsa, sai a wayigari a na cewa gara shi, a kan shugaba na yanzu. Misali, ba ma fata, wai kuma sai a ji a na fadin “gara Buhari da Tinubu”, ka da Allah Ya jiyar da mu wannan alkaba’i!!!.
Kaburin Bashi Ya Sabbaba Rashin Aiyukan-yi A Shekarun 1986, 1988 da 1989 A Nijeriya, IBB
Cikin Shekarar 1983, gabadaya bashin ketare “edternal debt” da ake bin Nijeriya, bai wuce dalar Amurka biliyan 17.8 ($ 17.8b) ba. Bayan da IBB ya dare karagar mulkin Kasar, cikin Shekarar 1991, sai bashin ya rikida ya zama dalar Amurka biliyan 33.3 ($ 33.3b) (CBN Economic and Financial Rebiew, Bol. 31 No 4 (kuoted in Omoruyi, 1993 : 401) ).
Sakamakon wancan tashin gwauron zabi da bashin na ketare ya yi a lokacin IBB, ya faru cewa, a tsakanin Shekarun 1986 da 1988 da kuma 1989, ma’aikatan hukumar jiragen kasa, da ma’aikatan kamfanonin fulawa, da ma’aikatan filayen jiragen kasa, da ma’aikatan kamfanonin gine gine da sauransu, kusan mutane sama da dubu 126 ne suka rasa aiyukansu a wannan Kasa (Fagge and Alabi, 2007 : 228).
Saboda ta’adar rayuwa da ruguntsumin tarkon basuka da Nijeriya ta tsinci kanta ciki a Shekarun 1989 da 1992, sai aka rika haduwa da zafafan zanga zanga tare da samun taho mu gama a tsakanin jama’a da kuma jami’an tsaro, wanda irin wannan yanayi na yamutsa hazo, shi ne babban abinda wadancan masu ba mu bashin ke son gani a tattare da mu. Ta irin wannan yamutsewar lamura ne za su kai ga samun damar shigowa cikin Kasar, kamar yadda labarai ke ta samun jama’a can wasu lokutan baya cewa, Turawan, na yunkurin kawo wata rundunar Soji cikin wannan Kasa, tare da yada zango a can jihar Sokoto, da sunan kwantar da tarzoma a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Sassaucin Basukan Na Sahale Daukar Dubban Ma’aikata A Kasa
Mai karatu na iya zama shaida cewa, kasantuwar lagon bashi na ketare da tsohon shugaban Kasa Obasanjo ya kassara, kamar yadda aka hakaito a baya cikin wannan rubutu, ya faru cewa, lokacin Obasanjon, gwamnati ta fi samun sukunin daukar dubban ma’aikata. Akwai ma wasu hukumomi iri iri da kafin zuwan Obasanjon babu su, amma ya zo ya kirkire su, tare da daukar dubban ma’aikata a karkashinsu.
A farko farkon wannan jamhuriyar siyasa ta hudu a wannan Kasa, har zuwa Shekarar 2011 a Kano, takardar daukar aiki na yin watangaririya ne a gari tamkar takardar tsire, ko takardar kunshe kosai a tsakanin jama’ar jihar. Amma, daga lokacin da Baba Buhari ya rika hadidiyar basuka a ciki da wajen wannan Kasa, irin wannan takardar aiki da a lokutan baya ta zamto gama gari tamkar awara, sai gashi an koma sayenta da tsabar kudi har naira dubu dari 500. A wasu lokutan ma, ta kan kai har kimanin naira miliyan guda da doriya ne.
Kunzumin basukan da shugaba Buhari ya rika hadidiya ba tare da kakkautawa ba, na daga silar kasa cikawa jama’ar Kasa wasu alkawura da yai musu tun a lokutan kamfen. Idan ba a manta ba, Buharin ya yi alkawarin samar da aiyukan yi guda miliyan uku ga ‘yan Kasa a duk Shekara. Mai karatu ya je ya binciki hukumar kididdiga ta Kasa, NBS da kuma kididdigar Bankin Duniya game da balahirar rashin aikin-yi a Nijeriya cewa, shin, a lokacin mulkin Buhari, batun samun aiyukan-yi, na ci gaba ne da habaka koko tabarbarewa ne?.
Tozon Bashin Kan Taka Rawa Ga Tsauwalar Farashin Man Fetur
Cikin Shekarar 2012, lokacin da tsohon shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ya tasamma cire tallafin man fetur “fuel subsidy”, wanda a lokacin farashin litar mai bai wuce naira 65 ne ba. Idan an janye tallafin, kudin litar guda zai zama naira 141 ne. Nan ne fa tsohon shugaban Kasa Buhari yai tsalle ya cane, tare da tunzura jama’ar Kasa har ta kai su ga yin wata zazzafar zanga zanga. Bugu da kari, Baba Buhari yake fadi cewa, ai ma naira 40 ne kawai ya dace a sayar da litar mai a Nijeriya. A takaice labari, tilas dole ne Jonathan ya hakura da batun janye tallafin na fetur.
Wani abu mai kama da almara koko laifi tudu ne, cikin Shekarar 2015, bayan Buhari ya sami nasarar shigewa cikin dutsen Aso “Aso Rock”, sai ga Buhari ya mayar da kudin litar man fetur naira 145. Kuma ba da jimawa ba ya cire tallafin na fetur. Ina maganar cewa, litar man feturin kyawonta naira 40 ne?. Har Goodluck ya sauka mulki a wannan Kasa, ba a taba sayar da litar mai a farashin naira 100 ba. Amma har kusan naira dari biyu an sayar da litar man fetur a gwamnatin Buhari. Babu shakka, tozon bashi a Kasa, na daga abubuwan da ke sabbaba shan litar mai da tsada!.
Idan mai karatu bai sha’afa ba, a can baya cikin wannan rubutu, an hakaito inda masu ba da bashi na ketare ke tilasa wadanda suka gaza biyan su bashi, na, su cire tallafin da suke sanyawa a bangarori muhimmai da ke amfanar rayuwar jama’ar Kasa. Irinsu fannin lafiya, ilmi, gona, har ma tallafin man fetur na shiga cikin lissafin. Ko a yanzu ma, gwamnatin Buhari ce ta janye tallafin man, tana dab da sauka daga mulki. A nan, ba a na magana ne game da mene ne alfanun cire tallafin na mai, koko barinsa ba? A na dai gabatar da alakar da ke tsakaninsa ne da kuma mummunar dalar bashi a Kasa illa iyaka.
Kadarori Da Kamfanonin Gwamnati Na Komawa Karkashin Mallakar Wasu Tsirarun Mutane Ne A Kasa
Lazim ne ga duk Kasar da ta ci mamakon basuka iya wuya, daga abubuwan da ke tasowa wannan Kasa a gaba shi ne, sayar da kadarori da kuma kamfanoni mallakar gwamnati ga wasu tsirarun mutanen da a zahiri ake kiransu da ‘yan kasuwa. Cikin rubutun baya, an gabatar da cewa, cikin Shekarar 2000 a Kasar Zambia, an yi irin wannan gwanjo na kadarorin hukuma ga ‘yan kasuwar Kasar. Haka ma a nan Nijeriya, mabanbantan hukumomi sun rika aiwatar da irin wannan ta’ada ta cefanar da kadarorin gwamnati daga lokaci zuwa lokaci, musamnan a cikin Shekarar 2002 zuwa 2004.
Irin wannan cefanar da kayan hukuma ko gwamnati da a wasu lokutan bashi ke bankara Kasa zuwa ga aikata hakan, ba safai ba ne ake yin irin waccan hada hada cikin yanayin da zai haifar da da mai ido a cikin Kasa ba, musamnan cikin Kasashe irin Nijeriya inda ta’adar cin hanci da rashawa ke samun tagomashi dare da rana.
A Nijeriyar, yayin cefanar da irin wadancan kadarori da aka ambata, sai a ga cewa, ai wasu tsirarun mutane shafaffu da mai a Kasar ne ke cin moriyar mallakar kadarorin. Kuma za a samu cewa, irin wadancan mutane hamshakai ne cikin gwamnatin Kasar. Ko su, ko ‘yan korensu ne ke kanainaye irin waccan hada hadar mallake kayan hukumar a duk sa’adda bukatar hakan ta taso. Bayan sayar musu da kadarorin, ma’aikatan hukuma da suka shafe tsawon Shekaru suna aiki a kamfanonin, da damansu na rasa aiyukansu ne daga lokacin da mallakar irin wadancan kamfanoni suka tashi daga karkashin gwamnati zuwa ga daidaikun mutane. Bugu da kari, kashi 10 (10%) na mu’amalar wannan saye da sayarwa na irin wadancan kadarori da doka ta aiyana cewa, ainahin ma’aikatan kamfanonin da aka cefanar ne za su amfana, nan ma dai sai dai su ji kida a magwan, ma’ana, za a tabar da sune daga cin moriyar wancan kashi 10 sananne a idon doka!. Mene ne ya faru ga dubban tsofaffin ma’aikatan kamfanin lantarki mallakar gwamnati na Kasa, da a wani lokaci can baya ake kiransa da NEPA bayan cefanar da shi ga ‘yan kasuwa?. A wasu Kasashe masu tsarki daga rashawa sabanin Nijeriya, za a samu cewa, bayan cefanar da kamfanonin, suna mikewa ne a ci gaba da hada hadar arziki, fiye ma da lokacin da suke jibge karkashin mallakar gwamnati.
Ba ya ga cefanar da wadancan kadarorin hukuma karkashin kuskundar cin hanci da rashawa a Nijeriya, yanzu kuma an fara mika ikon ci gaba da gudanar da wasu kadarorin gwamnatin Kasar ne karkashin kulawar wasu manya manyan kamfanonin ‘yan jari hujja da suka mamaye Duniya ido rufe, da sunan samun riba ninkin ba ninkin ta kowace hanya! Sanannen abu ne cewa, gwamnatin Baba Buhari, ta mika filayen jiragen Malam Aminu Kano da na Dr Nnamdi Azikwe zuwa ga hannun wani hamshakin kamfani a kasar Amurka, wanda karkashin kulawarsa da ikonsa ne wadancan filayen jirage za su ci gaba da mirginawa ta fuskar tattalin arziki maimakon hukuma. Daya daga filayen jiragen, zai shafe tsawon Shekaru 20 ne karkashin yarjejeniyar. Daya kuwa, zai shafe tsawon Shekaru 30 ne. Da sunan wai Nijeriya za ta sami mamakon kudaden shiga daga wancan kamfani ba’amurken da zai ci gaba da ikon gudanar da mirginawar filayen jiragen biyu.