A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Xi ya yi nuni da cewa, duniya na bukatar kyakkyawar dangantaka tsakanin Sin da Amurka, kana ko kasashen biyu za su iya samun hanyar da ta dace don daidaita alakarsu, hakan na iya shafar makomar daukacin bil-Adama.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, har yanzu hakan ba zai taba iya magance matsalolin da Amurka ke fuskanta ba ko kuma kalubalen da duniya ke fuskanta. Bai dace wani bangare ya yi kokarin siffanta daya bangaren bisa son ransa, kuma har yanzu ya hana daya bangaren hakkinsa na samun ci gaba ba.
Xi ya ce, a ko da yaushe kasar Sin na fatan ganin alakar Sin da Amurka mai dorewa, ya kuma yi imanin cewa, manyan kasashen biyu za su iya shawo kan matsaloli daban-daban, da lalubo hanyar da ta dace ta yin sulhu bisa mutunta juna, da zaman lafiya da hadin gwiwa tare da samun moriyar juna, yana mai kira ga bangaren Amurka da ya rungumi dabi’ar nuna sanin ya kamata, da yin aiki tare da kasar Sin a cikin harkokin kasa da kasa.
A nasa bangare kuwa, Blinken ya isar da gaisuwar shugaba Biden ga shugaba Xi Jinping, yana mai cewa, Amurka na mutunta alkawuran da shugaba Biden ya yi, ba ta neman “sabon yakin cacar baka”, ba ta neman sauya tsarin kasar Sin, ba ta neman adawa da kasar Sin ta hanyar karfafa kawance, kana ba ta goyon bayan “‘yancin kai na yankin Taiwan”. Amurka ba ta da niyyar yin rikici da kasar Sin, kuma tana fatan yin mu’amala mai zurfi tsakanin manyan jami’an ta da kasar Sin, da kiyaye hanyoyin tattaunawa marasa shinge, da warware bambance-bambancen dake tsakaninsu, da neman tattaunawa, da yin musaya da hadin gwiwa. (Ibrahim)