Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 da ke Jihar Bauchi ta tura Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa ‘raini ga kotu’ har zuwa nan da wata daya.
Alkalin kotun, Malam Hussaini Turaki, shi ne ya aike da babban malamin zuwa gidan gyara halinka a zaman kotun da ya gudana ranar Litinin.
A kwafin umurnin aikewa da Malamin gidan yari da wakilinmu ya ci karo da ita da ke nuni da cewa bisa ga ‘raini ga kotu’ wato ‘Contempt of court’ ne Alkalin ya aike da malamin gidan yari, inda za a da dawo da shi gaban kotun a ranar 19 ga watan gobe.
Umurnin da Alkalin ya bai wa babban jami’in kula da gidan yarin na cewa, “An baka izinin ka karbe shi ka tsare shi a gadirum sai an aiko maka da wata oda.”
Umarnin na kotun ya ce idan har ba wata umarnin na daban kuma aka aiko ba, malamin zai cigaba da zama a gidan har zuwa ranar 19/07/2023.
Idan za a tuna dai, a ranar Laraba 31 ga watan Mayun 2023 ne dai Alkalin kotun ya umarci jami’an tsaro da su kamo malamin a duk inda suka gan shi sakamakon kin bayyana a gaban kotu.
Sai dai a zaman kotun a ranar 5 ga watan Yuni malamin ya bayyana a gaban alkalin inda lauyoyinsa suka gabatar da rahoton likita da ke cewa bai zo kotun ba ne sakamakon rashin lafiya da ke fama da ita.
Bayan da lauyoyin nasa suka gabatar da rahoton, sun roki kotun da ta janye tare da jingine umarnin da ta bayar na farko na cewa a kamo malamin duk aka gan shi. Sai dai Alkalin ya daga zaman zuwa yau don yanke hukunci kan bukatar.
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan hukunci, daya daga cikin Lauyoyin malamin, Barista Kamal A. R Muhammad, ya ce, su na nazarin halin da ake ciki domin daukan matakin da ya dace na nema wa malamin ‘yanci.
A cewarsa: “Da farko an dawo kotun ne domin a saurari bukatarmu na neman a kori karar saboda da hujjarmu na cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar. Na biyu kuma akwai rokon da muka yi na cewa umarnin da kotun ta yi a ranar farko na a nemo malam a tsareshi saboda bai zo kotu ba a jingine don mun gabatar da rahoton asibiti da ke cewa baya da lafiya.
“Kafin yau din ma, mun shigar da daukaka kara da muke neman a canza shari’ar zuwa wata kotu da take da hurumi zuwa gaban alkalin da ke da hurumi, sai Alkalin ya ce ba zai kori karar ba don yana da hurumin sauraron wannan karar.”
A cewar Lauyan, “Yanzu dai halin da ake ciki Alkalin ya ce a kai Malam zuwa gidan yari har zuwa ranar 19 ba watan Yulin 2023.”
Barista Kamal malamin ya ce akwai matakan da za su dauka na nuna korafinsu kan wannan lamarin.
LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa, tun da farko dai, ‘yansanda ne suka fara gabatar da malamin a kotun majistire bisa zarginsa da laifin tada zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiyan al’umma, lamarin da ya kai ga zuwansa gidan yari na tsawon mako guda amma daga bisani ya samu beli.
Kodayake ma’aikatar shari’a ta Jihar Bauchi ta amshi ragamar shari’ar daga baya.
Sai dai kuma bayan fitowarsa ne aka sake mayar da shari’ar da ake masa daga kotun majistiren zuwa kotun shari’ar Musulunci.
Wakilinmu ya ce, zuwa yanzu haka dai malamin wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi na tsare a babban gidan gyara halin da ke Bauchi.