A baya bayan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da Eric Domb, mamallakin gidan zoo mai suna “Pairi Daiza”, kuma dan kasar Belgium ya aike masa, inda cikin martaninsa, shugaba Xi ya ce yana fatan a matsayinsa na abokin kasar Sin, mista Domb zai ba da gudummawar da ta dace wajen ingiza bunkasar kawancen Sin da Belgium, da na Sin da nahiyar Turai baki daya.
Kafin hakan, cikin wasikarsa ga shugaban na Sin, mista Eric Domb ya ce ba za a iya cimma nasarar bunkasa dangantakar Sin da Belgium ba, har sai an yi aiki tukuru na tsawon lokaci, tare da sadaukarwa tsakanin kawayen kasashen biyu daga dukkanin fannonin rayuwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp