Hukumar tattara kudaden haraji da raba kudaden da kuma tsimi da tanadin kasafin kudi (RMAFC) ta amince da karin kashi 114 na albashin zababbun shugabanni ‘yan siyasa da suka hada da shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, gwamnoni, ‘yan majalisa da ma’aikatan shari’a da na gwamnati.
RMAFC itace ke da alhakin tantance albashin da ya dace ga masu rike da mukaman siyasa da suka hada da Shugaban kasa, Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni, Mataimakan Gwamnoni, Ministoci, Kwamishinoni, Masu Ba da Shawara na Musamman, ‘Yan Majalisa da masu rike da ofisoshi kamar yadda aka tanada a sashe na 84 da 124 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.
Hukumar ta bukaci majalisun dokokin jihohi 36 da su gaggauta yin gyare-gyare kan dokokin da suka dace don ba da damar sake duba tsarin albashin masu rike da mukaman siyasa, shari’a da na gwamnati.
Shugaban RMAFC, Muhammadu Shehu wanda kwamishiniyar tarayya Rakiya Tanko-Ayuba ta wakilta ce ta yi wannan kiran a wajen gabatar da rahoton gyare-gyaren tsarin albashin ga gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, a ranar Talata a Birnin Kebbi.