Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta cafke wani dan shekara 30 bisa zarginsa da kokarin kisan kai ta hanyar banka wa wata karamar yarinya wuta.
Ya zargi yarinyar da cewa ita mayya ce don haka ne ya cinna mata wuta bayan takun-sakar da ya shiga tsakaninsu.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Wani Sabon Hari A Kogi
- An Bayyana Ranar Buga El Clasico Tsakanin Real Madrid Da Barcelona
A sanarwar manema labarai da kakakin rundunar, Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, ya ce an kama mutumin ne bisa zargin yunkurin kisan kai da azabtar da karamar yarinyar.
Wanda ake zargin ya bayyana abin da ya faru a matsayin tsautsayin ya rutsa da ita, Hafsat Bala a ranar 18 ga watan Yuni a gidansa da ke yankin Rafin Albasa da ke Bauchi.
“Shi ya tambaye ta me ya kawota cikin gidansa, sai ta ce masa yayarta ce ta aikota domin ta kashe shi. Shi wanda ake zargin ya yi kokarin fitar da ita daga cikin gidan, amma yarinyar ta ki, tare da ikirarin cewa yarinyar ta ce an bukaci ta birne wasu layu a kusurwar gidan.”
A cewar sanarwar, wanda ake tuhumar ya roki yarinyar da ta cire dukkanin abubuwan da ta ce ta burne a gidan amma ta ki.
“Kwatsam hakan ya fusata wanda ake zargin, a nan ne ya debo kalanzir ya banka mata wuta da shi a cikin gidan kan zargin cewa ita mayya ce.”
A cewar Wakil lokacin da ‘yansanda suka samu rahoton faruwar lamarin sun garzaya bisa jagorancin babban baturen yanki domin ceto yarinyar zuwa asibitin koyarwa na ATBUTH.
Wakil ya kara da cewa bincikensu na ci gaba da gudana kuma za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.