Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya tsige sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke jiharsa, inda ya umurce su da su mika al’amuran ofisoshinsu ga babban jami’i a kananan hukumominsu.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar a daren Laraba, ta ce, an tsige sakatarorin ilimin nan take.
Hakan ya biyo bayan zaman da aka yi a ranar Laraba a kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Sokoto, wadda ta bukaci shugaban makarantar Town Model Primary School da ke Sabon Birni da ke karkashin karamar hukumar Sabon Birni, Ibrahim Abdullahi, ya ba da shaida kan karar da dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Sa’idu Umar ya gabatar a gaban kotun yana kalubalantar cancantar mataimakin gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na tsayawa takarar gwamna a zaben 2023.
Umar a cikin karar da ya gabatar, ya na kalubalantar cancantar abokin takarar gwamna a jam’iyyar APC, Mohammed Idris Gobir, kan cewa bai halarci makarantar firamare ba.
Sbugaban makarantar ya samu rakiyar Lauyan Sa’idu Umar, S.I. Ameh SAN, zuwa zaman sauraron karar don bayarda shaida tare da gabatar da takardar shaidar shiga makarantar a 1981 da na kammala karatu a shekarar 1987, don tabbatar da cewa Gobir bai halarci makarantar ba kamar yadda ya yi ikirari.
Shugaban zaman sauraron kararrakin zaben, Mai shari’a Haruna Mshelia, ya amince da kwafin takardun da aka gabatar masa yayin da babban lauyan wadanda ake kara, Cif Jecob Ochidi, ya ki amincewa da takardun.
Korar da Ahmad Aliyu ya yi wa sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jim kadan bayan kammala zaman kotun, ana kallon hukuncin a matsayin ramuwar gayya da riga-kafi ga irin wannan sheda a kotun zabe, domin shi ma Gwamnan yana fuskantar irin wannan kara ta rashin halartar makaranta a kotun.