Babbar Kotun Majistire da ke Minna ta zartar da hukuncin daurin zaman gidan yari na tsawon shekara 22 ga wani jami’in Dan-sanda mai mukamin Insifekta, Gbenga Fajuyi bisa kamasa da laifin yin ciki wa diyarsa mai shekara 13 a duniya tare da hallaka sabon jaririn da ta haifa.
Fajuyi mai shekara 47 a duniya yana aiki ne a karkashin hukumar ‘yansanda da ke jihar Neja, kotun ta kamasa da laifuka guda uku da suka hada da fyade da keta haddi, lalata zuri’a da kisan kai.
Da take yanke hukuncin, Alkalin kotun babbar Majistire, Christy Barau ta misalta wanda ta daure a matsayin wani babban abun tsaron da ya kasance a maimakon ya kare rayuwar diyarsa karama har zuwa lokacin da za ta zama babbar mace sai ya zama shi ne mai illata mata rayuwa.
Ta ce, laifuka uku da ta kama shi da aikatawa sun saba wa sashi na 18 karamin sashi na 2 na dokar kare hakkin yara ta jihar Neja na shekarar 2010 da sashi na 390 karamin sashi 25, da sashi na 397 B na manyan laifuka ta Final kod.