Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai bar Abuja a yau Talata zuwa ziyarar aiki kasar Portugal bisa gayyatar da shugaban kasar, Marcelo Rebelo de Sousa, ya yi masa, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.
Shugaban wanda zai yi wata tattaunawa a hukumance da takwaransa na Portugal, za kuma a ba shi lambar yabo ta kasa da kuma yi masa ado da ‘Great Collar of the Order of Prince Henry’.
- Buhari Ya Rantsar Da Ariwoola A Matsayin Sabon Alkalin Alkalai Na Kasa
- Buhari Ya Ce Ba Zai Nemi Wa’adi Na Uku Ba
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya sanya wa hannu a ranar Talata, ta ce ana sa ran shugabannin biyu za su jagoranci wani gagarumin taron kasashen biyu da kulla wasu yarjeniyoyin da suka shafi kan iyakokin kasashen biyu.
Shugaba Buhari zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar Portugal inda zai tattauna da shugabanta Dr Augusto Santo Silva da kuma firaministan kasar Portugal Antonio Costa.
Shehu ya bayyana cewa, a yayin ziyarar, shugaban kasar zai yi jawabi a wani taron ‘yan kasuwan Nijeriya da na kasar Portugal tare da yin ganawa daban-daban da wasu zababbun manyan jami’an gudanarwa na kasar Portugal da masu son zuba jari a Nijeriya.
Shugaba Buhari zai kuma halarci taron Majalisar Dinkin Duniya a kan teku, wanda aka fara a Lisbon a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni, wanda zai gudana har zuwa 1 ga watan Yuli.
Taron, wanda gwamnatocin Kenya da Portugal suka shirya tare da goyon bayan Sashen Tattalin Arziki da Al’uma na Majalisar Ɗinkin Duniya (DESA), na da nufin hanzarta ɗaukar sabbin hanyoyin samar da sabbin hanyoyin kimiyya don fuskantar ƙalubalen da ke fuskantar teku da kuma yanayin ruwa na duniya.
Ana kuma sa ran shugaban na Nijeriya zai tattauna da ‘yan Nijeriya mazauna kasar Portugal kan al’amuran da suka shafe su da kuma abubuwan da ke faruwa a cikin gida.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo sai Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da kuma Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami.
Sauran sun hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj-Gen Babagana Monguno (rtd) da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) Honorabul Abike Dabiri-Erewa.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban zai koma Abuja ranar Asabar 2 ga watan Yuli.