Dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea dan asalin kasar Senegal Kalidou Koulibaly ya yarda da yarjejeniyar da zata sa ya koma kungiyar Al Hilal ta kasar Saudi Arabia da taka leda.
Koulibaly wanda ya koma Chelsea daga Ssc Napoli ta kasar Italiya a bara ya buga wa Chelsea kwallaye 23 a bana inda ya jefa kwallaye biyu a raga.
Koulibaly ya fadi a shafinsa Na Twitter cewar babbar nasara ce a gareshi ya saka rigar Chelsea kuma ya godewa mahunkunta da magoya bayan kungiyar akan soyayyar da suka nuna masa a tsawon zaman nasa a Stamford Bridge
Al Hilal ta dauki manyan yan wasa a bana daga Firimiya Lig da suka hada da Ruben Neves na kungiyar Wolverhampton Wanderes
Chelsea na neman rabuwa da wasu daga cikin yan wasanta domin samun damar dauko sabbin jini
Zuwa yanzu Yan wasa 4 sun bar kungiyar da suka hada da Kai Harvertz, Ngolo Kante da Kalidou Koulibaly yayinda ake cinikin Mason Mount da Mai tsaron raga Edouard Mendy