Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da hutun mako guda ga daliban makarantun Firamare da Sakandare domin gudanar da bukukuwan sallar idin layya a jihar.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mukaddashin babban sakataren ma’aikatar ilimi, Ya’u Jibrin, wadda jaridar LEADERSHIP ta samu kwafinta a ranar Lahadi.
“An ba da wannan hutun ne na mako guda ga daukacin Makarantun Gwamnati da masu zaman kansu a fadin Jihar daga ranar Litinin 26 ga watan Yuni zuwa Litinin 3 ga Yuli, 2023,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, ana sa ran daliban makarantar kwana za su koma makarantun su a ranar Lahadi 2 ga Yuli, 2023.
Sabida haka, ma’aikatar ilimi ta na yi wa daukacin ma’aikata da dalibai barka da Sallah.