Babban Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC), Farfesa Abubakar Rasheed, ya yi murabus bisa radin kansa domin ci gaba da koyarwa a Jami’ar Bayero Kano (BUK), inda daman a nan yake aka nada shi wannan mukamin.
Farfesa Rasheed, wanda ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin a Abuja, ya ce ya shafe shekaru bakwai a matsayin babban sakataren hukumar.
- NUC Ta Daga Darajar Kwalejin Sa’adatu Rimi Zuwa Jami’a A Kano
- NUC Ta Bankado Haramtattun Jami’o’in Digiri 49 A Nijeriya
Sanarwar murabus din Rasheed ta biyo bayan amincewa da bayar da lasisin ga jami’a ta uku mallakar jihar Kogi.
Sabuwar jami’ar zata kasance a Karamar hukumar Kabba dake jihar.
Da yake gabatar da takardar amincewa ga gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a Abuja ranar Litinin, sakataren zartarwa na NUC, Abubakar Rasheed, ya ce jami’ar za ta kasance jami’a ta 62 mallakar gwamnatin jihar a fadin kasar nan.
Rasheed ya sanar da Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) na kafa wannan Jami’a.
Ya ce, “A madadin Hukumar, daga ranar 26 ga watan Yuni, 2023, Jami’ar Jihar Kogi ta Kabba an amince da ita a matsayin jami’a 62 mallakar gwamnatin Jiha a kasar.”
Ya bayyana sabuwar jami’ar a matsayin aikinsa na karshe a Hukumar, bayan da ya ba da izini ga jami’o’in kasar da dama a tsawon mulkinsa na shekaru bakwai.
Tun da farko Gwamna Bello ya ce an aika da kudirin kafa jami’ar
Majalisar dokokin Kogi ta zama doka.
Gwamnan wanda ya ce abi hanyoyin kafa sabuwar jami’ar, ya kuma bayyana fatan cewa zata fara daukar daliba kafin wa’adinsa ya kare.