‘Yan bindiga sun afka gidan wani shugaban ‘yan sintiri Mallam Nabanje da ke karamar hukumar Danmusa a Jihar Katsina, inda suka hallaka shi har lahira sannan suka kuma yi wa matansa fyade.
Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun fito ne domin farautar Mallam Nabanje wanda kuma ya kasance, shi ne shugaban ‘yan sintirin yankin.
- Da Buhari Ya Cire Tallafin Mai Da Tinubu Bai Zama Shugaban Kasa Ba —Garba Shehu
- Mahajjata Sama Da Miliyan 2 Ne Za Su Yi Aikin Hajjin Bana
‘Yan bidigar dai suna zargin marigayin ne bisa lalata wasu maboyarsu a ‘yan kwanamin baya.
Lamarin ya auku ne a makon da ya gabata, bayan da ‘yan bindigar dauke da makamai suka kutsa yankin suka far harbe wasu mutanen da ke yankin.
Wasu mazuna yankin biyu sun samu raunukan a harin, inda suka yi amfani da damar kai harin suka sace mata uku wadanda daga baya suka sako su.
A cewar majiayar, a lokacin da ‘yan bindigar suka isa yankin sun wuce kai tsaye zuwa gidan Mallam Nabanje, inda suka iske shi zaune a inuwar wata bishiya sai suka fara musayar wuta da shi bayan albarusan sun kare ne sai marigayin ya ruga zuwa cikin wani kango sai suka zagaye shi suka yi masa yankan Rago.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Sadiq Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya sanar da cewa, bayan da rahoton lamarin ya riske rundunar, an yi gaggawar tura ‘yansanda zuwa yankin.
Ya ce, rundunar na kokarin farautar ‘yan bindigar da suka aikata ta’asar.