A jiya ne, kasar Sin ta karyata kalaman karya da wasu kasashe suka yi game da dokar tsaron kasa na yankin musamman na Hong Kong (HKSAR).
Da yake jawabi a yayin zaman kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 53, wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin tana matukar adawa da duk wata kasa ko makiya daga ketare dake neman tsoma baki a harkokin cikin gida da na tsarin shari’arta ta hanyar fakewa da batun kare hakkin bil-Adama.
A cewar wakilin na Sin, tun lokacin da aka fara aiwatar da dokar tsaron kasa, yankin musamman na Hong Kong ya shiga wani sabon mataki, daga yanki mai fama da hargitsi a baya zuwa yanki mai bin tsarin mulki da wadata. Yana mai cewa, an sake jaddada bin doka da oda, kuma an fi kare ’yancin mazauna Hong Kong yadda ya kamata.
Ya kara da cewa, dokar ta ba da tabbacin martaba doka da ’yanci na shari’a a yankin musamman na Hong Kong, kuma kotuna suna gudanar da shari’o’insu ba tare da tsangwama ba. (Ibrahim Yaya)