A yau Talata ne ministan kula da harkokin cinikayya na kasar Sin Wang Wentao, ya mika daftarin amincewa da yarjejeniyar tallafin kamun kifi ga darakta janar ta hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO), Ngozi Okonjo Iweala, a birnin Tianjin na arewacin kasar Sin.
Yarjejeniyar wadda WTO ta gabatar yayin taron ministocin kasashe mambobinta karo na 12 a watan Yunin 2022, ita ce irinta na farko da WTO ta gabatar da zummar tabbatar da cimma burin kare muhallin mai dorewa. Yarjejeniyar za ta fara aiki a hukumance ne bayan ta samu amincewa daga kaso 2 bisa 3 na mambobin WTO. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp