A jiya Talata ne aka bude taron sabbin jagororin dandalin raya tattalin arziki na duniya karo na 14, ko taron Davos a birnin Tianjin na arewacin kasar Sin.
Taron na wannan karo dai ya hallara baki daga sassan gwamnatoci, da masu zaman kansu kimanin 1500 daga sama da kasashe da yankunan duniya 90. Kaza lika da yawa daga mahalartansa sun bayyana kwarin gwiwarsu ga makoma, da kuma karsashin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.
Da yake tsokaci yayin zaman dandalin, babban manajan kamfanin Danfoss mai hada-hadar makamashi dake birnin Tianjin Dai Jian, ya ce dandalin Davos na lokacin zafi, ya samar da damar tattaunawa, da musaya tsakanin sassan ’yan siyasa, da ’yan kasuwa na kasashe daban daban, tare da baiwa sauran sassan duniya karin karfin gwiwa, ga yadda kasar Sin ke ci gaba da kyautata tsarinta na bude kofa.
A bana ne ake ciki shekaru 10 da kaddamar da shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, manufar dake kunshe da gaskiyar niyya, da tafiya tare da kasashen Afirka bisa adalci, da salo na yin daidai, da cimma moriya.
A nasa tsokacin kuwa, manajan daraktan bankin Standard, banki mafi girma a nahiyar Afirka mai helkwata a Afirka ta kudu Philip Mayborough, cewa ya yi ci gaban tattalin arzikin kasar Sin muhimmin dalili ne da ya kamata a yi la’akari da shi wajen tallafawa bunkasar nahiyar Afirka a cikin gida, kuma tuni kasashen Afirka da Sin suka cimma manyan nasarorin hadin gwiwa karkashin cinikayyar albarkatun gona. (Saminu Alhassan)