Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng ya ce, a shirye Sin take ta samar da sabbin damarmaki ga Afrika ta hanyar zamanantar da kanta da samun ingantaccen ci gaba. Haka kuma, za ta zurfafa tare da kara karfin hadin gwiwa mai muhimmanci dake tsakanin bangarorin biyu.
Han Zheng ya bayyana haka ne a yau Alhamis, yayin da yake jawabi ga bikin bude baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afrika karo na uku a Changsha, babban birnin lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin.
Bugu da kari, Mr. Han Zheng ya gana da shugaba Lazarus Chakwera na kasar Malawi, da takwaransa na tsibirin Zanzibar na Tanzania Hussein Ali Mwinyi, a jiya Laraba a birnin Changsha na lardin Hunan.
Shugabannin sun gana ne yayin baje kolin harkokin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na 3, wanda ke gudana yanzu haka a birnin na Changsha.
Yayin zantawar mataimakin shugaban kasar Sin da mista Chakwera, Han ya ce Sin da Malawi abokai ne dake neman ci gaba tare, wadanda kuma suke goyawa juna baya tare da amincewa juna. Ya ce karkashin kulawa da jagorancin shugabannin kasashen 2, Sin da Malawi sun ci gajiyar kyakkyawar alaka bisa daidaito, kana sun samu ci gaban hadin gwiwa mai ma’ana.
Yayin da yake zantawa da shugaba Mwinyi kuwa, Han ya ce kasar sa da Tanzania abokan arziki ne, kuma ’yan uwa dake hulda tare. Kaza lika kawancen hadin gwiwa tsakanin Sin da Zanzibar na da matukar muhimmanci wajen raya dangantakar sassan 2.
Har ila yau, hadin gwiwar Sin da Tanzania na samun kyakkyawan ci gaba, wanda ya kara karfafa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin sassan 2. (Masu Fassara: Fa’iza Mustapha, Saminu Alhassan)