Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, HAJIYA HADIZA UMAR NAMADI DAN MODI, ta tattauna da wasu tsirarrun jaridu ciki har da LEADERSHIP HAUSA, a karon farko tun bayan rantsar da maigidan nata a matsayin sabon gwamnan jihar.A tattaunawar da yayi da ita, ta yi bayanai masu fa’ida da suka shafi niyyarta ta hidimta wa al’ummar Jihar Jigawa domin kara bunkasa ci gaban jihar da kyautata rayuwarsu. Wakilinmu, MUSTAPHA IBRAHIM KANO, ya tattauna da ita ga yadda tattaunawar tasu ta kasance.:
Da farko, ranki ya dade za mu so mu ji sunanki da tarihin ki?
To Alhamdu lillahi Sunana Hadiza Umar Namadi Dan Modi, mai dakin gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar Namadi, Masha Allah an haife ni a karamar hukumar kafin Hausa cikin Jihar jigawa a nan ne kuma nayi makarantar firamare,da karamar sakandire daga aji daya zuwa uku, daga gare mu ne aka fara tsarin 6,3,3,4 a lokacin mu kuma daga nan ne na ci jarabawar makarantar kimiyya ta `Yanmata da ke Birniwa, Daga can sai babbar makarantar `Yanmata ta kimiyya ta Jahon wato GGSSS Jahon.Da na kammala ta ne sai aka yi mani aure to daga nan ban samu damar ci gaba da karatu ba sai daga baya na tafi Kaduna,Can ne, na yi makarantar gudanarwa ta Management Science na samu Diploma a Caps a Kaduna, Cooperate Studies daga nan ne kuma sai na je jami`ar Bayero ta kano BUK na yi karatun Digirin farko bangaren kasuwanci, sai Digiri na biyu shi ma duk a jami’ar Bayero.Na yi karatun kwarewa na ilimin gudanarwa kan dan Adam w Allah ya albarkace ni da `ya`ya Alhamdulillah, wannan shi ne takaitaccen tarihi na.
Me za ki ce akan zaben Mallam Umar Namadi Dan Modi da kuma rantsar da shi a matsayin gwamnan Jihar Jigawa a karshen watan da ya gabata?
Da farko dai mu na godewa Allah madaukakin Sarki da jama`ar JIhar jigawa wadanda saboda zaben da suka yi ne Allah yasa aka samu nasara a lokacin, aika masu sakon fatan alkairi kan gudummawar da suka ba mu hadin kai tun daga zaben mu, har zuwa rantsuwa a ranar 29 ga watan Mayu 2023.da ta gabata har zuwa yau da mu ke magana a wannan wuri na gidan gwamnatin Jihar jigawa, inaso al`umma mu sani cewa shi shugabanci ba abu ne na alfahari ba, ba abu ne na kece raini ba ! da sanya Gwalagwalai ba ne ko Azurfa ba ne da dai sauran su.Ba abu ne na nuna isa da sa kaya masu tsada ba, da yin takama, Ni ina tunanin shugabanci abu ne na taimakawa al`umma su samu Ilimi,
Al`umma suna son a inganta rayuwarsu sai kuma bayan an san matsalolinsu,daganan sai a gane irin hanyar data dace a taimaka masu. Taimakawar bata wuce su samu fita daga cikin matsalolin da suke fuskanta
An ce duk inda ka ga Namiji ya samu nasara to akwai gudummawar matarsa kamar yadda ita ma haka abin ya ke, wane irin goyan baya za ki ba shi a matsayin ki na matarsa?
Da farko dai zamu roki Allah kar ya barmu mu yi rayuwa a kan son zuciyar mu, zan fadawa jama`a su ta ya mu da addu`a saboda shugabanci amana ne, ranar da za`a rantsar da shi, sai da aka kira ni nazo kusa da shi ya karbi rantsuwa da Alkawari na rike amanar al`ummarsa haka kuma a ranar hisabi ranar kiyama zamu kasance da shi saboda wannan dalili ya zama dole ne mace ta fadawa mijinta gaskiya domin kamar yadda na fada a baya shugabanci ba abIn alfahari ba ne, ba abIn ado da sutura ba ne, ba abin huce-takaicii ba ne,ba na ayi takama ba ne,ni dai na san idan mutum yayi kokarin iya kar iyawar sa Allah zai taimake shi ya samu nasara, to wannan shi ne irin tsari na da burina na goyan bayan da zan bawa wannan bawan Allah.
Kasancewar kina wurin aka yi rantsar da shi nan take ya ce baya son a kira shi da Edcellency menene ra`ayin ki kan wannan manufarsa?
Ra`ayina a kan wannan manufarsa shi ne abin haka ya ke domin wannan yana nuna cewa da ba mu ne akan mulkin ba wasu ne suke yi har Allah ya kawo wa`adin saukar su,su ka sauka haka muma watarana,mu ma za mu tafi wasu su zo su hau mulkin saboda haka ne ya yi tunanin cewa ka da muyi dabi`ar masu mulki da son mulki, da kuma son girma, da son cewa shi daban ne yake da sauran mutane,shi yasa ya ce ka da ma a kira shi da suna ‘Edcellency’. Saboda idan yau shi ne gwamnan jigawa watarana idan Allah yaso da rai da lafiya, sai ka ga ba shi ba ne ba,wannan matakin da ya dauka na cewa kada mulki ya shiga ransa domin wata rana zai gushe kaga ya yi rigakafi ke nan ka tuna ance rugakafi ya fi magani, abu ne mai kyau da mutum zai tsira da mutuncinsa, amma idan ba ka yi haka ba, har mulki ya shiga ranka idan ma ba kayi haka ba har jama`a su ka cusa ma son mulki wani abu ne a ranka, to dole sai ka yi shi a rayuwa wanda hakan zai iya sa ka shiga rikici da alumma. Daukar mataki na cire san mulki da girman kai da ya yi a wannan rana ni dai ina tare da shi, da goyon bayan shi kan wannan ra`ayi nasa cire sunan mai girma gwamna ina tare da shi.
Na san dai Jihar Jigawa na daga cikin jihohi da aka ce akwai talauci kuma wannan yasa yara da mata na cikin masu rasa ransu a lokacin haihuwa kina da rawar takawa wajen maganin wannan matsala a matsayin na matar gwamnan jigawa?
Alhamdu lillah, na ji dadin wannan tambaya da aka yi mani domin ko babu komai mahaifina Malamin Asibiti ne ina kuma da sha`awar yin wannan aiki na kulawa da lafiyar al’umma musamman ma matsalolin mata da kan rasa rayukan su a lokacin haihuwa,da cututtukan da kan addabi mata da kananan yara, da rashin abinci mai gina jiki da sauran su na daga cikin abtbuwan da zan bawa mahimmanci, da yin aiki tukuru na ganin an kawar da wannan matsalar a Jihar jigawa ko kuma a rage tu.
To ya ya kika ji da kika kasance a matsayin matar gwamna?
Koda yake kafin wannan ya ruke makamai daban-daban kamar kwamishina kuma ya zama mataimakin gwamna duk a wannan lokaci ma sha Allah. Amma abin lura a nan shi ne, a ce Allah ya kaddara ma a littafin ka na rayuwa cewa kai shugaba ne ba karamar rahama ba ce amma abin roko daga jama`ar Jihar jigawa da ma sauran al`umma, shi ne su taimake mu da addu`a na cewa mu da Allah ya ba mu wannan dama kada mu yarda mu bi son ran mu, domin idan mutum ya bi san ran shi sai ya shiga wani halin da bai dace ba amma idan bai bi ta son ran shi ba sai Allah ya taimake shi, y agama komai lafiya,wannan ita ce gaskiyar al’amari saboda haka Allah yasa wannan mulki ya zama alkairi duniya da lahira a gare mu da al’ummar Jihar jigawa baki daya.