Daga ranar 1 ga watan Yuli, dokar kasar Sin ta hulda da kasashen waje za ta fara aiki a hukumance. Wannan ita ce shiryayyar doka irinta ta farko kan huldar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da kasashen waje, wadda ta samar da cikakken tubali bisa doka ga yadda kasar Sin za ta yi musaya da kasashen waje.
Dokar za ta ba duniya damar kara fahimtar kasar Sin da ra’ayin kasar na inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya da kuduri da hakkin dake wuyan Sin na kare cikakken ‘yanci da yankuna da tsaro da muradunta na ci gaba dama tabbatar da adalci da daidaito a duniya.
Makasudin samar da wannan doka shi ne, fayyace matsayin kasar Sin kan huldar kasa da kasa, da inganta tsare-tsaren kasar masu ruwa da tsaki a mu’amalarta, da ketare da bayyana jajircewar Sin kan tabbatar da zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa da moriyar juna ga duniya, bisa doron doka.
Haka kuma da samar da ka’idojin dokar na raya dangantakar Sin da ketare, da inganta hadin kan kasa da kasa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)