Shugaban kasar Malawi, Lazarus McCarthy Chakwera, ya bayyana a wata hira da manema labarai a ranar 30 ga watan Yuni cewa, zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Malawi da Sin za su taimaka wa Malawi wajen samun ci gaba mai ‘yancin da dorewa, da bin hanyar raya kasa da ta dace.
Ya ce, bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da Afrika, a matsayin wani muhimmin dandali na zurfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, ya bai wa sassan biyu damar kulla alaka tsakanin jama’a, da masana’antu, da gwamnatoci.
Bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya na kasar Sin da Afirka karo na uku na gudana ne a birnin Changsha, inda Malawi take halartar bikin bisa matsayin babbar bakuwa. (Mai fassara : Yahaya)