Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa Alhazan Nijeriya 14 sun rasu a kasar Saudiyya daga fara gudanar da aikin hajjin na shekarar 2023 zuwa yanzu.
Shugaban kula da sashen aiyuka kuma shugaban kungiyar likitocin NAHCON na Nijeriya Dr. Usman Galadima, ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar bayan Arafat da masu ruwa da tsaki a ranar Lahadi a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
- Saudiyya Ta Tsare Mutum 17,000 Da Suka Yi Yunkurin Hajji Ba Tare Da Izini Ba
- Hajj 2023: NAHCON Ta Cancanci Yabo Da Jinjina Ba Kushe Ba – Almakura
Galadima ya bayyana cewa mahajjata bakwai sun rasu kafin Arafat, shida kuma sun rasu a cikin kwanaki biyar na Mashair (manyan ranakun aikin Hajji) sannan karin mutum daya ya rasu bayan Arafat.
“Mun sami rahoton mutuwar mutane shida a Mashair, hudu sun mutu a Arafat, sauran biyun kuma sun mutu a Mina. Tuni mun rasa mahajjata bakwai kafin Arafat kuma a yanzu haka an sanar da ni cewa mun rasa wani alhaji. Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa 14.
“Yawan mace-mace yayi kama da na 2019,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa, tawagar likitocin ta samu rahoton bullar cuta ga wasu Alhazai guda uku a lokacin aikin hajji kuma nan da nan aka kwashe alhazan da suka kamu da cutar don yi musu rigakafin kamuwa da cutar.
Galadima ya kuma bayyana cewa, tawagar ta samu rahotan haifuwa biyu a lokacin aikin hajji a Mina, Arafat da Muzdalifah, inda ya kara da cewa daya daga cikin mata masu juna biyu ta haihu a kan hanya, yayin da ta biyu kuma a asibiti.
Ya kuma jaddada bukatar yin cikakken binciken likitocin kafin aikin hajji tare da bayar da takardar shaidar lafiya mai inganci.
Ya kuma ce ya kamata a hana tsofaffin alhazai da masu fama da rashin lafiya shiga wurin jifan shaidan a Jamrat saboda damuwar da ke tattare da hakan.
A nasa jawabin shugaban hukumar ta NAHCON, Alhaji Goni Sanda, ya bayyana cewa za a fara jigilar maniyyata zuwa Nijeriya ne a ranar Talata 4 ga watan Yuli.