‘Yansandan Afganistan a ranar Litinin sun kama wasu masu garkuwa da mutane bakwai tare da kubutar da wani mutum da aka yi garkuwa da su a kudancin lardin Helmand.
Daraktan yada labarai da al’adu na lardin a cikin wata sanarwa ya ce “Jami’an ‘yan sandan lardin sun kaddamar da wasu ayyuka na musamman.
- Wani Abun Fashewa Ya Tarwatse A Wani Masallaci Ya Kashe Akalla Mutane 18 A Afganistan
- Gwamnatin Taliban Ta Haramtawa Mata Yin Aiki
“Rundunar ‘Yansanda sun kama wasu mutum bakwai da ke da hannu wajen sace wani mutum mai suna Nimatullah Bin Gul Mohammad, a gundumar Musa Qala ta lardin.”
A wani samame makamancin haka da safiyar ranar Lahadi, jami’an ‘yan sanda sun cafke wasu mutane hudu da ake zargin suna da hannu wajen sata da karbar kudi a babban birnin kasar Kabul, a cewar hedkwatar ‘yan sandan Kabul.
A wani bangare na shirin gwamnati na tabbatar da doka da oda, ma’aikatar harkokin cikin gida ta kara tsaurara matakan murkushe masu aikata laifuka da masu dauke da makamai a kasar.