Allah ya yi wa ministan Abuja ma farko, Cif Mobolaji Ajose-Adeogun rasuwa.
Ya rasu yana da shekaru 96.
- Tinubu Ya Yi Ganawarsa Ta Farko Da Hafsoshin Tsaro
- Hajjin Bana: Abin Da Ya Sa Alhazan Nijeriya 14 Suka Rasu
Majiya daga iyalansa ta ce Cif Ajose-Adeogun ya rasu ne a ranar Asabar 1 ga Yuli, 2023.
Marigayin dai kwararre ne a fannin man fetur da iskar gas, ya yi tasirin da ba za a manta da shi ba a harkar kadarori a Nijeriya.
Ya kasance ministan farko na babban birnin tarayya, Abuja.
Ajose-Adeogun ya yi fice a Kamfanin Raya Man Fetur na Shell kuma ya zama Kwamishinan hadin gwiwa da wadata na Tarayya a 1975 sannan kuma ya zama Kwamishinan ayyuka na musamman a Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya bayan ya yi ritaya.
Daga baya a shekarar 1976, lokacin da aka kafa babban birnin tarayya, Cif Ajose-Adeogun ya zama Minista na farko.
Ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki.