A yau Litinin ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na taya Saliyo murnar gudanar da babban zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.
An rawaito kwamitin gudanar da zaben kasar ta Saliyo na sanar da sakamakon babban zaben na ranar 27 ga watan Yuni, inda ya ce dan takarar jam’iyya mai rike da mulki, kuma shugaban kasar mai ci Julius Maada Bio ne ya lashe babban zaben da yawan kuri’u har kaso 56.71 bisa dari na jimillar kuri’o’un da aka kada, kuma tuni ya sha rantsuwar kama aiki.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, tun bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Saliyo cikin shekaru 52 da suka gabata, bisa kokarin bangarorin biyu, an dade da karfafawa, da kuma zurfafawa dangantakarsu. Har ila yau, bangaren Sin zai ci gaba da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu a dukkan fannoni kamar yadda ya yi a baya, tare kuma da inganta ci gaban dangantakar Sin da Saliyo. (Safiyah Ma)