• English
  • Business News
Wednesday, October 29, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Me Manufar Argentina Ta Fara Biyan Bashin Waje Da Kudin Sin Rmb Ke Nufi?

by CMG Hausa
2 years ago
Rmb

A ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata ne kasar Argentina, ta yi amfani da damarta ta asusun lamuni na duniya IMF, wadda ta tanadi biyan bashi a tsarin musamman na SDR, da amfani da kudin Sin RMB wajen biyan bashin kasashen wajen da IMF ke bin ta, wadanda suka kai dalar Amurka biliyan 2.7. 

Wannan ne karon farko da Argentina ta yi amfani da kudin Sin RMB wajen biyan bashin waje. Kaza lika a jajiberin ranar, babban bankin kasar ya sanar da sanya kudin din RMB cikin jerin kudaden da zai rika ta’ammali da su, tare da ajiyar su cikin tsarin hada hadar kudaden kasar, kana ya amince cibiyoyin hada hadar kudi na kasuwancin kasar su bude asusun ajiya na RMB.

  • Bangaren Sin Ya Taya Saliyo Murnar Gudanar Da Babban Zabe Cikin Kwanciyar Hankali Da Lumana 

Game da hakan, shugaban babban bankin kasar Miguel Ángel Pesce, ya ce kamar sauran kasashen duniya, Argentina ta jima da yin imani ga makomar hada hadar kudi ta kasa da kasa ta amfani da kudin na kasar Sin.

Argentina ta dade tana fama da matsalar bashin kasashen waje, wanda ke da nasaba da karfin dalar Amurka. A matsayin ta na kasa ta uku mafi karfin tattalin arziki a Latin Amurka, matakin da Argentina ta dauka ya zama wani abun misali. Don kuwa a halin yanzu, bisa kokarin Brazil, da Argentina da wasu kasashe, sauran kasashen yankin Latin Amurka sun gabatar da tunaninsu na “cire tasirin dala”.

Game da hakan, shugaban Venezuela Nicolás MADURO Moros ya bayyana cewa, kamata ya yi a fara gudanar da aikin kawar da babban karfin dala. Kaza lika shi ma shugaban Bolivia Luis Alberto Arce Catacora, ya ce za a tattauna yiwuwar yin amfani da RMB yayin gudanar da cinikayya. Duk wadannan sun bayyana burin kasashe masu tasowa masu yawa, wajen cimma bambancin harkar kudade, da kuma daukar hanyar ci gaba mai zaman kanta.(Saminu Alhassan, Safiyah Ma)

LABARAI MASU NASABA

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa
Daga Birnin Sin

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba
Daga Birnin Sin

Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Kara Bude Kofa Da Karfafa Daidaita Dabarun Samar Da Ci Gaba

October 28, 2025
Next Post
Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Binciken Mukaman Karshe Na Tambuwal

Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Binciken Mukaman Karshe Na Tambuwal

LABARAI MASU NASABA

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

COAS Shaibu Ya Sha Alwashin Murƙushe ‘Yan Ta’addar Lakurawa 

October 29, 2025
Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

Binciken ‘Yan Sanda Kan Wanda Ake Zargi Da Tawayen “‘Yancin Kan Taiwan” Mataki Ne Na Adalci Don Kare Hadin Kan Kasa

October 29, 2025
Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

Afuwar Tinubu Ga Fursunoni: Saura Ƙasa Da Shekaru 6 Maryam Sanda Ta Shaƙi Iskar ‘Yanci

October 29, 2025
Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

Xi Jinping Zai Gana Da Donald Trump

October 29, 2025
Gwamnatin Rikon Kwarya: Shirin DSS Ne Na Damke Atiku Da Peter Obi Kafin Rantsar Da Tinubu

DSS Ta Kama Wani Matashi Da Ya Yi Kira A Yi Juyin Mulki A Kafofin Sada Zumunta

October 29, 2025
An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

An Kashe Ɗan Sanda Da Ɗan Hakimi A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Gombe

October 29, 2025
Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

Ribadu Ya Gargaɗi ‘Yan Siyasa Kan Tayar Da Hankali A Zaɓen Anambra

October 29, 2025
ADC Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Kan Amfani da Zargin Juyin Mulki Wajen Yaƙar ‘Yan Adawa

Ba Matakan Tinubu Ne Suka Karyar Da Farashin Kayan Abinci Ba – ADC

October 29, 2025
‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sanya Wa Majalisa Bam – Ɗan Majalisa

October 29, 2025
Sanusi Ga ‘Yan Nijeriya: Ku Dora Wa Buhari Alhakin Matsatsin Tattalin Arziki Ba Tinubu Ba

Tsoron Boko Haram Ne Ya Sa Jonathan Ya Fasa Cire Tallafin Man Fetur – Sanusi II

October 29, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.