Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari da aka dakatar.
Kyari, wanda ke tsare tun bayan kama shi a shekarar 2022, an bayar da belinsa ne a ranar Alhamis.
- Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Abba Kyari Ta Dakatar Da Bincikensa
- Ana Wata-ga-wata: Gwamnati Ta Sake Bankado Kadarorin Abba Kyari
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta bayyana cewa ana neman tsohon babban dan sandan ne da zargin hannu a cinikin badakalar hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.
Daga nan aka kama shi aka gurfanar da shi a gaban kotu, inda kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Rundunar ‘yan sandan dai ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda tsohon shugaban IRT na ‘yan sanda ya aikata.
Daga bisani an dakatar da shi daga aikin.
A ranar Alhamis ne mai shari’a Kolawole Omotosho na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da belinsa bisa wasu sharudda masu tsauri.
Sai dai kuma har yanzu Kyari na da shari’a a gaban mai shari’a Emeka Nwite na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.