Bisa gayyatar da aka yi masa, firaministan kasar Mongoliya Luvsannamsrai Oyun-Erdene, ya halarci taron Davos na bazara karo na 14 a birnin Tianjin, da kuma ziyarar aiki a kasar Sin a kwanan baya.
A yayin ziyararsa a kasar Sin, Oyun-Erdene ya zanta da manema labaru na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG a takaice, inda ya yaba da ra’ayin kasar Sin na zaman jituwa da amincewa da bambanci, da kuma yadda kasar ke kokarin cika alkawarin da ta dauka.
Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Mongoliya ba. Kaza lika kasar Sin tana jurewa da mutunta yadda sauran kasashe ke zabar tsarin siyasa daban-daban, da kuma rike ra’ayi da matsayi daban-daban, amma dole ne su mutunta juna da zama tare. Wannan muhimmin ra’ayi ne da kasar Sin ta amince da shi.
A dayan hannu kuma, kasar Sin ta dauki manufofi masu dorewa, tana kuma yin alkawuran dake hade da hakikanin abubuwa na zahiri. Ana iya takaita hakan da jimla daya, wato ‘darajar cika alkawari ta kai zinari dubu’, domin ba karya ko yaudara a kudurorin ta.
Bugu da kari, ya kamata mu ga cewa, kasashen duniya za su iya yin imani da cewa, Sin da Asiya suna da karfin inganta ci gaban tattalin arzikin duniya, tare da sa kaimi ga ci gaban dukkan bil’adama. (Mai fassara: Bilkisu Xin)