Kungiyar Muslim Media Watch Group of Nigeria (MMWG) ta bukaci shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu da ya yi watsi da kiran tattaunawa da ‘yan bindiga.
Kungiyar ta bayyana Kiraye-kirayen zaman tattaunawa da gwamnati da ‘yan ta’adda da Sanata Ahmed Sani da Sheikh Ahmed Gumi suka yi a matsayin ‘mara amfani’ kuma ba za a amince da su ba.
- Sulhu Da ‘Yan bindiga Ne Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Nijeriya – Yerima
- ‘Yansanda Sun Fatattaki ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane 21 Da Shanu 20 A Katsina
A maimakon haka, kungiyar MMWG a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kodinetan ta na kasa, Alhaji Abdullahi Ibrahim, da aka rabawa manema labarai a Ilorin, jihar Kwara, ta bukaci Tinubu da ya dora wa sabbin shugabannin tsaro da aka nada nauyin fito da dabarun karya lagon ‘Yan ta’adda a fadin kasarnan.
“Akwai bukatar shugaban kasa ya baiwa jami’an tsaro wa’adin da ya kamata su kawo karshen rashin tsaro a Nijeriya da sanya ido a kan yadda ake amfani da kason kudin da ake ba su.
Ya kara da cewa duk wanda ya nemi a tattauna da masu aikata laifuka da kuma yin afuwa ga ‘yan ta’adda, to ba su yi tunani mai kyau ba, don haka kungiyar bata goyon bayan irin wadannan kiraye-kirayen.