Gwamnatin jihar Kano ta kammala shirin daukar nauyin dalibai 1,100 da za su kammala karatun digiri a jami’o’in cikin gida da na ketare.
Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, Dokta Yusuf Kofar-Mata ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Talata a Kano.
- Tinubu Ya Bada Umarnin Binciko Wadanda Suke Kashe-Kashe A Filato
- Kotu Ta Hana INEC Gurfanar Da Kwamishinan Zaben Adamawa
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewar gwamnatin jihar ta sanar da bude tantancewar masu digiri na farko da za su iya neman gurbin karatu a jami’o’in gida da waje.
Kofar-Mata, ya ce gwamnatin jihar ta kaddamar da kwamitin mutum tara domin tantance masu neman gurbin karatun.
“Mun karbi sakamakon dalibai 1,200 kuma an tantance sama da 800.
“Za a dauki nauyin dalibai dubu daya da dari daya a rukunin farko. Kwamitin na ci gaba da aikin tantance daliban.
“Wannan na cikin manufar da gwamnatin Gwamna Abba Kabir-Yusuf ta yi, na ba wai ‘yan asalin jihar Kano dama domin samun damar samun sabbin sana’o’i,” in ji shi.
Kofar-Mata ya ce, kwamitin na kokarin ganin an samar da wadanda suka yi nasara a fannonin karatu na musamman da na kasa da kasa domin magance matsalar ilimi a jihar.
“Bayan kammala karatunsu da yawa daga cikin daliban za su dawo da dabarun kasuwanci da sauran damammaki da za su tallafa da inganta harkokin kasuwanci masu zaman kansu da za su bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa baki daya,” in ji shi.