A wata mai zuwa, za a cika shekaru biyu da Amurka ta janye sojojinta daga kasar Afghanistan. A ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2021, jirgin soja na karshe na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman birnin Kabul, wanda ya dasa aya ga yakin Afghanistan da aka kwashe tsawon shekaru 20 ana yinsa.
A kwanakin baya, majalisar harkokin wajen kasar Amurka ta fitar da wani rahoto na tantance matakan da Amurka ta dauka na janye sojojinta daga Afghanistan, wanda ya yi suka game da yanayi na rashin tsari da oda wajen kwashe sojojin, amma ba tare da bayyana ainihin abubuwan da ya kamata gwamnatin Amurka ta yi tunani a kansu ba.
Kaddamar da yaki a kan wata kasa mai mulkin kanta abu ne da ya keta dokokin kasa da kasa, amma me ya sa rahoton bai yi bayani a kansa ba? Dubun dubatar fararen hula sun halaka ko jikkata a sakamakon yakin na tsawon shekaru 20, baya ga tabarbarewar yanayin tsaro da zaman lafiya a yankin, me ya sa rahoton bai yi bayani a kansa ba? Amurka ta fake da sunan “wanzar da dimokuradiyya” wajen tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe, amma me ya sa rahoton bai yi bayani a kansa ba?
Duk da cewa Amurka ta janye sojojinta daga Afghasnitan, amma har yanzu tana kakabawa kasar takunkumin tattalin arziki, tare da kwace kudade daga al’ummar kasar, matakan da suka jefa kasar cikin matsalolin jin kai.
Ba shakka, al’ummar duniya ba za su yi na’am da rahoton ba.
Amurka na daukar kanta a matsayin misali wajen kare hakkin dan Adam da dimokuradiyya, amma ga abin da ta haifar a Afghanistan da ma sauran sassan duniya. Idan ba ta daina daukar matakai na nuna fin karfi da ma gyara yadda take tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe yadda ta ga dama ba, to, ba shakka, abin da ya faru a Afghanistan zai ci gaba da faruwa a sassan duniya. (Mai Zane:Mustapha Bulama)