Gwamnatin tarayya ta ce ta shigar da masu bukata ta musanman 500 cikin tsarin inshorar lafiya na kasa (NHIS), don inganta kiwon lafiyarsu.
Babban sakataren ma’aikatar jin kai na kasa, Dakta Sani Gwarzo, ne ya bayyana hakan a wani taron rabon katin NHIS ga wadanda suka amfana da shirin a Larabar nan a Abuja.
- KECHEMA Ta Kaddamar Da Kwamitin Bayar Da Gudunmawar Kula Da Kiwon Lafiya A Kebbi
- Muhimmancin Kafa Cibiyar Kulawa Da Lafiyar Hakori
A cewarsa, matakin zai tabbatar da samar da kiwon lafiya mai sauki ga nakasassu a fadin kasar nan.
Talla
Gwarzo ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawagarsa zuwa shugaban masu bukata ta musanman da ke Karo a Abuja.
Talla