‘Yan majalisar wakilai na neman a sake duba albashinsu da alawus-alawus din da ake biyansu, biyo bayan cire tallafin man fetur da kuma halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki a halin yanzu.
Kamfanin dillacin labarai (NAN), ta ruwaito cewa bukatar hakan na zuwa ne bayan zaman da ‘yan majalisar suka yi a ranar 11.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Neja Ta Umarci Masu Gidaje A Hanyoyin Ruwa Su Tashi
- Mark Zuckerberg Ya Fara Daukar Horo Don Yin Dambe Da Elon Musk
Koken ‘yan majalisar ne ya tilastawa majalisar yin zama don tattauna batun.
Sun kuma bukaci shugaban majalisar, Tajudeen Abass, da musu karin haske kan dalilin da ya sa aka jinkirta biyansu albashi da alawus-alawus dinsu na watan Yuni.
Daya daga cikin ‘yan majalisar da ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana kan zaman majalisar zartarwa ba, ya ce sun yi maganar karin albashi ne kawai ban da batun jinkirin biyansu.
Dan majalisar ya ce sun sanar da shugaban majalisar cewar kudaden da ake biyansu a yanzu ba zai isa biyan bukatunsu ba.
“Babu wanda ya yi magana kan wasu kudi ko an biya mu ko ba a biya mu ba,” in ji shi.
Majiyar ta ce sun bukaci karin albashin ne duba da yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki.
Sai dai shugaban majalisar a yanzu bai yi musu alkawarin samun karin albashi ko alawus-alawus ba, saboda a cewarsa lamarin na bukatar gyara a cikin kasafin kudi.